Shugaban NITDA ya takalo yaki da Malaman Jami’a, ana barazanar karbe masa Digiri

Shugaban NITDA ya takalo yaki da Malaman Jami’a, ana barazanar karbe masa Digiri

  • Kungiyar malaman jami’a na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ta gargadi shugaban NITDA
  • Shugaban ASUU ya bukaci Kashifu Inuwa ya janye kalaman da ya yi a kan rashin ingancin UTAS
  • Abin har ya kai kungiyar malaman su na cewa za a bukaci a karbe shaidar digirin da aka ba Inuwa

Bauchi - Kungiyar malaman jami’a na reshen jami’ar Abubakar Tafawa Balewa a jihar Bauchi, tana yi wa shugaban NITDA, Kashifu Inuwa, barazana.

Rahoton da ya fito daga jaridar Punch a yammacin Alhamis ya bayyana cewa kungiyar ASUU ta na maganar karbe digirin da aka ba Mal. Kashifu Inuwa.

Malaman jami’ar sun cin ma wannan matsaya ne bayan Kashifu Inuwa ya gabatar da rahoto da ya nuna cewa manhajar UTAS ta fadi gwajin da aka yi.

ASUU ta kirkiri wannan manhaja ta UTAS ne a madadin IPPIS domin a rika biyansu albashi. Amma sai aka ji NITDA na cewa ba za a iya aiki da ita ba.

Kara karanta wannan

Yadda zan jagoranci jam'iyyar APC ta samu nasara a 2023. Sanata Adamu ya magantu

NITDA ta yi karya a kan UTAS - ASUU

Shugabannin kungiyar malaman jami’ar ATBU sun fitar da jawabi mai taken “UTAS da karyayyakin NITDA” domin yin raddi ga shugaban hukumar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin da suka fitar, ‘Yan ASUU sun shaidawa manema labarai cewa akwai bukatar Kashifu Inuwa ya janye kalamansa, ya fadi gaskiya a kan manhajar.

Shugaban NITDA
Kashifu Inuwa tare da Isa Ali Pantami Hoto: @NITDANigeria
Asali: Twitter

Independent ta rahoto shugaban ASUU na ATBU, Ibrahim Inuwa ya na cewa idan Inuwa bai lashe amansa ba, zai zama dole a nemi a soke digirin da aka ba shi.

Ibrahim Inuwa ya ce a kan tsayawa gaskiya ne jami’ar ATBU ta ba shi shaidar digirinsa tun farko. A cewarsa, shugaban NITDA ya san gaskiyar lamarin UTAS.

Gwamnati na yaki da manhajar UTAS

ASUU ta kuma ce ba tayi mamakin ganin yadda jami’an gwamnati irinsu Ministan sadarwa da shugaban hukumar NITDA ke kokarin ganin bayan UTAS ba.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Goyon bayan Buhari, sanin siyasa da abubuwa 4 da suka taimakawa Adamu

“ASUU ta reshen jami’ar ATBU ta na takaicin cewa ita ce ta yaye Ministan sadarwa, Isa Ali Pantami da shugaban NITDA, Kashifu Inuwa."
“Jami’ar da ta yi suna wajen yin abin da ya kamata wajen koyarwa da bada tarbiya. Ministan sadarwa ya raba ofishinsa da son ran zuciyarsa.”

- Ibrahim Inuwa

A karshe kungiyar ASUU ta ce ta na zargin saboda an bankado cewa ba a bi doka wajen ba Ministan matsayin Farfesa ba ne yake adawa ga manhajar.

Rikicin ASUU da El-Rufai

Kwanaki ASUU ta yi zama a kan filin ABU Zaria da Nasir El-Rufai yake neman karbewa da karfi da yaji, har aka kawo maganar a karbe digirorin da aka ba shi.

Gwamnan na jihar Kaduna El-Rufai ya samu shaidar B. Sc da MBA duk daga jami'ar ABU Zaria kusan shekaru 40 da suka wuce baya ga karatu da ya yi a ketare.

Kara karanta wannan

Duk da Shugaban kasa ya sa baki, har yanzu APC na fama da rikicin cikin gida a jihohi

Asali: Legit.ng

Online view pixel