Harin Abuja-Kaduna: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Gwamnati Ta Yi Don Kawo Karshen Rashin Tsaro, Saraki

Harin Abuja-Kaduna: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Gwamnati Ta Yi Don Kawo Karshen Rashin Tsaro, Saraki

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Abubakar Bukola Saraki, ya lissafo abubuwa 5 da ya kamata gwamnati ta yi don kawo karshen rashin tsaro
  • Ya zayyano abubuwa 5 din ne a shafukansa na Facebook da Instagram inda ya tsamo su cikin hanyoyin kawo tsaro 20 da majalisar tarayya ta 8 ta mika wa gwamnati
  • Hakan ya biyo bayan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai cikin sa’o’i 96 a filin jirgin sama da harin da suka kai wa jiragen kasa inda suka halaka jama’a

Tsohon shugaban majalisar tarayya, Dr Abubakar Bukola Saraki, ya lissafo abubuwa 5 wadanda gwamnatin tarayya za ta yi don kawo karshen rashin tsaro a kasar nan, rahoton Nigerian Tribune.

Ya bayyana matakan ne ta shafinsa na Twitter da Instagram wanda ya tsamo su cikin hanyoyi 20 da majalisar dattawa ta 8 ta tanadar wacce ta gabatar wa gwamnati.

Kara karanta wannan

Yadda Jami’an tsaro suka yi burus duk da an samu rahoton za a kai wa jirgin kasa hari

Harin Abuja-Kaduna: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Gwamnati Ta Yi Don Kawo Karshen Rashin Tsaro, Saraki
Harin Abuja-Kaduna: Abubuwa 5 Da Ya Kamata FG Ta Yi Don Kawo Karshen Rashin Tsaro, Saraki. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Twitter

Ya nuna rashin jindadinsa dangane da hare-haren da aka kai tashar jirgin sama da kuma jiragen kasa inda suka halaka mutane da dama yayin da suka raunana wasu.

Ya ce asarar rayukan da aka yi ya yi yawa, hakan ya sa ya lissafo abubuwan da ya dace gwamnati ta yi don kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.

Ga matakai 5 din da ya lissafo

1. Sarki ya ce akwai bukatar samar da jami’an tsaron hadin guiwa don kawo karshen ‘yan bindigan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kuma wajibi ne su yi gaggawar fara aiki, sannan jami’an ne zasu samar da salon da za a bi don kawo karshen ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.

2. Wajibi ne shugabannin tsaro biyu su zauna don kawo hanyar da za su bullo da ita don samun hadin guiwa cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, sun kashe 9 a jihar Neja

Wajibi ne a kawo karshen wannan rashin hadin kan da ke tsakanin jami’an tsaronmu cikin gaggawa, su dunkule wuri guda.

3. Dole ne mu inganta hanyoyin dakatar da matsaloli na tsaro ta hanyar amfani da salo da fasahar zamani.

Wajibi ne mu yi amfani da kimiyya wurin gano yadda ‘yan ta’adda suke gudanar da ayyukansu sannan a samar da makaman zamani ga jami’an tsaro don gudun ci gaban hare-hare.

4. Ba daga zaune zamu dunkule mu gano yadda suke kai hare-hare ba. Wajibi ne mu yi amfani da bayanan sirri. Hakan zai ba mu damar kawo karshen makiyanmu cikin sauri.

5. Wajibi ne mu nuna karfin gwamnatin tarayya don tabbatar da ‘yan sandan Najeriya, ‘yan sandan farin kaya da sojoji sun gano kuma sun yi aiki da hanyoyin kawo karshen hare-haren nan.

Nigerian Tribune ta ruwaito yadda Saraki ya ce:

“Babu yadda za a yi a ci gaba da rayuwa a haka. An kai wa mutane 970 hari a jirgin kasa tsakanin Katari da Rijana. Wajibi ne a kawo karshen duk wadannan matsalolin.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel