Gwamnatin Buhari za ta saya wa NDLEA na'urar gane mutum idan ya sharara karya

Gwamnatin Buhari za ta saya wa NDLEA na'urar gane mutum idan ya sharara karya

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana amincewarta ga sayo na'urorin gano karya da gilashin hangen nesa ga hukumar NDLEA
  • Wannan na zuwa ne daga zaman majalisar zartaswa ta tarayya da aka yi a yau dinnan a gidan gwamnati
  • Gwamnati ta bayyana cewa, akalla Naira biliyan daya za a kashe domin sayen wadannan na'urori

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da cire zunzurutun kudi har Naira biliyan 1 don siyan na’urar gane karya da gilashin hangen nesa cikin dare ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Laraba a Abuja bayan taron na FEC na mako-mako, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hasashen Shehu Sani: Abubuwan da Abba Kyari zai yi gamo dasu a magarkamar Kuje

Gwamnati za ta sayi na'urar gano karya da gilashin gani cikin dare ga 'yan NDLEA
Gwamnatin Buhari za ta saya wa NDLEA na'urar gane mutum idan ya sharara karya | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Ministan wanda ya yaba da ayyukan hukumar ta NDLEA ya ce an dauki matakin ne domin dakile safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Hukumar NDLEA a karkashin sabon shugabancinta ta yi nasarar kamawa tare da gurfanar da gungun 'yan harkallar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga cikin wadanda hukumar ta kama a baya-bayan nan har da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, wanda ake zargi da taimakawa wajen shigar da miyagun kwayoyi da kuma gudanar da harkallar kwayoyi ta kasa da kasa.

Sauran fitattun wadanda ake zargi a hannun hukumar sun hada da wani basaraken gargajiya da wani malamin addini da aka kama a filin jirgin sama.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shi yana bayyana dalilin sayen wadannan na'urori, musamman gilashin gani da dare:

“Wannan daidai yake da karin na’urar fasaha da ake nufin tallafawa ayyukan NDLEA na dare bisa la’akari da karfinta na tallafawa ganin NDLEA cikin dare."

Kara karanta wannan

Kudin Paris Club: Kotu ta yi watsi da wata kara da jihohi 36 suka shigar kan gwamnatin Buhari

NDLEA sun yi kokari, abin a yaba: Kungiya ta fadi me ya kamata a yiwa Abba Kyari

A wani labarin. kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Writers Association of Nigeria (HURIWA), a ranar Litinin, ta yabawa hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa bisa yadda ta fifita aiki fiye da son rai da kishin aljihu.

Kungiyar ta yabawa NDLEA karkashin jagorancin shugabanta Buba Marwa, saboda ayyana neman DCP Abba Kyari, bisa zargin alaka da safarar miyagun kwayoyi, Punch ta ruwaito.

A yau ne sanarwa ta iso Legit.ng Hausa cewa, NDLEA ta ayyana neman Abba Kyari bisa zarginsa da kokarin kulla harkallar safarar miyagun kwayoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel