Rikici: Kotu Ta Dakatar Da Ganduje Daga Rushe Shugabancin KACCIMA

Rikici: Kotu Ta Dakatar Da Ganduje Daga Rushe Shugabancin KACCIMA

  • Wata kotun tarayya da ke Jihar Kano wacce alkali Jane Esienanwan Inyang ta yi hukunci, ta dakatar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga rushe shugabancin KACCIMA
  • An samu rahoto akan yadda gwamnan ya bayar da umarnin rushe shugabancin cibiyar sakamakon rikicin da ya ke ta ruruwa a cikinta
  • Dama ya kamata wa’adin shugaban cibiyar, Alhaji Dalhatu Abubakar ya kare ne tun watan Oktoban 2021, daga nan rikici ya dinga barkewa

Kano - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kano, wacce alkali Jane Esienanwan Inyang ta yi hukunci ta dakatar da gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje daga rushe shugabancin cibiyar kasuwanci, masana’antu, ma’adanai da noma ta Jihar Kano, KACCIMA,

Har ila yau, kotun ta kara da dakatar da gwamnan da sauran wadanda ake kara daga nada Alhaji Lawan Sule Garo da Ambasada Muntari Gashash a matsayin kwamitin rikon kwarya na cibiyar kasuwancin Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Sokoto: Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin ba tsagin Sani nasara

Rikici: Kotu Ta Dakatar Da Ganduje Daga Rushe Shugabancin KACCIMA
Kotu Ta Dakatar Da Ganduje Daga Rushe Shugabancin Hukumar KACCIMA. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya bayar da umarnin rushe shugabancin cibiyar tun bayan yadda rikici ya dinga ruruwa a cikinta.

Wa’adin shugaban cibiyar, Alhaji Dalhatu Abubakar ya kare ne tun watan Oktoban 2021 tun bayan nan hayaniya ta dinga tashi, daga wannan sai wata.

Ba Ganduje kadai aka maka kotun ba

Wata kara wacce lauyan Usman H Darma da sauran masu shigar da kara guda biyu, suka shigar mai kwanan wata 14 ga watan Maris na 2022 da 21 ga watan Maris na 2022, kotun ta umarci bangarorin biyu da su dakata daga rushe shugabancin da kuma nada shugabannin rikon mwarya har sai an kammala sauraron karar.

Cikin masu karar akwai Usman H Darma mai kara na farko, Umar Isma’il Umar, mai kara na biyu da kuma cibiyar kasuwanci, masana’antu, ma’adanai da noma a matsayin mai kara na uku, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

EFCC ta saki tsohon gwamna bayan kwashe kwana 6 a hannunta, ta kwace fasfotinsa

Wadanda ake karar sun hada da Alhaji Lawan Sule Garo (na farko) Ambasada Muntari Gashash na biyu, Gwamna Jihar Kano, Antoni janar na Jihar Kano da kuma kwamishinan ‘yan sanda a matsayin na hudu da na biyar.

Gwamna Ganduje ya mika mulki hannun mataimakinsa, ya shilla kasar waje

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya miƙa mulkin Kano hannun mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ganduje ya yi haka ne jim kaɗam kafin ɗagawar Jirginsa zuwa haɗaɗɗiyar daular larabawa (UAE) ranar Laraba a Abuja.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Laraba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel