Yajin Aikin ASUU: Ba Za Mu Bar Titunan Abuja Ba Har Sai An Buɗe Makarantu, 'Kungiyar NANS

Yajin Aikin ASUU: Ba Za Mu Bar Titunan Abuja Ba Har Sai An Buɗe Makarantu, 'Kungiyar NANS

  • Daliban Najeriya karkashin kungiyar NANS za su cigaba da yin zanga-zanga a titunan Abuja kan yajin aikin da ASUU ke yi
  • Sunday Asefon, shugaban kungiyar daliban, NANS, ya ce ba za su dena zanga-zangar ba har sai an bude dukkan jami'o'in da ke kasar
  • A cewarsa, tunda an rufe ajujuwansu na makaranta, za su mayar da titunan Abuja ajujuwansu har zuwa lokacin da aka bude makarantun

FCT, Abuja - Kungiyar Daliban Najeriya, NANS, a ranar Litinin ta cigaba da zanga-zangar ta na neman ganin an kawo karshen yakin aikin da kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, ke yi.

Da ya ke magana a yayin zanga-zangar a Abuja, shugaban NANS na kasa, Sunday Asefon, ya ce daliban a shirye suke su fito su mamaye manyan titunan Abuja, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnati: Har yanzu ba a san adadin mutanen da harin jirgin kasa Abuja-Kaduna ya shafa ba

Yajin Aikin ASUU: Za Mu Cigaba Da Mamaye Manyan Titunan Abuja, Har Sai An Bude Makarantu, NANS.
Yajin Aikin ASUU: NANS za ta cigaba da zanga-zanga a Abuja. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Mun gaji, ba mu damu da abin da zai faru ba sakamakon zanga-zangar, Shugaban NANS

Ya kara da cewa daliban sun gaji kuma ba za su fasa abin da suka fara ba har zai an bude dukkan jami'o'i a kasar.

Asefon ya ce:

"Tunda sun kore mu daga ajujuwan mu za mu mayar da titunan Abuja dakunan karatun mu.
"Wannan ba wasan yara bane, da gaske muke yi a yanzu. Sakon mu mai sauki ne: A bude mana jami'o'in mu. Mun tabbatar idan ba a janye yakin aikin nan ba, Daliban Najeriya ba za su bar tituna ba.
"Za mu koma titunan ba tare da damuwa da abin da zai faru ba. Mutanen Abuja su sani cewa za mu mamaye manyan titunan a matsayin wani mataki na ganin an bude makarantun mu."

Kara karanta wannan

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Abin da Shugaban Kungiyar Dalibai na Jami'ar Tarayya ta Dutse, FUD ya ce game da zanga-zangar

Wakilin Legit.ng Hausa ya tuntubi Muhammad Mukhtar Umar, shugaban kungiyar dalibai na Jami'ar Tarayya ta Dutse, FUD, domin jin ra'ayinsa kan zanga-zangan da NANs ta cigaba da yi a Abuja.

Kalamansa:

"Da farko, ina son in jinjina wa NANS saboda kokarin da suke yi babu gajiyawa don ganin daliban Najeriya sun koma aji.
"Kaga, zanga-zangar da NANS ke yi ya zama dole ne domin dukkan mu mun yi imanin shine abinda gwamnati ta ke fahimta sosai, yawaitan yajin aikin yana shafar daliban mu ta hanyoyi da dama."

Da aka yi wa Mukhtar Umar tambaya shin ko dalibansu na tare da masu zanga-zangar, ya kada baki ya ce:

"Eh, dukkan mu muna tare da masu yin zanga-zangan na lumana, duk da cewa ban samu halartan wurin da kai na ba a ranar da aka fara domin na yi wa daliban mu rakiya Legas wurin wasannin NUGA.
"Yanzu kowa ya san inda matsalar ta ke, Nagode."

Asali: Legit.ng

Online view pixel