Zamfara da Borno sun zama sakaru, sun lashe gasar karatun Alkur'ani Izu 60

Zamfara da Borno sun zama sakaru, sun lashe gasar karatun Alkur'ani Izu 60

  • Ɗalibai daga jihohin Arewa biyu ne suka samu nasarar lashe kyautar zaƙaƙurai a gasar ƙaratun Alƙur'ani izu 60
  • Mutum biyu daga ɓangaren Mata da Maza waɗan da suka lashe Miliyan N3m kowane sun fito ne daga Zamfara da Ka Borno
  • Mutum sama da 300 ne suka fafata a rukunonin gasar da dama da suka haɗa da Izu 60, 40 har da Izu 10

Bauchi - Abba Goni-Mukhtar daga jihar Borno da kuma Haulatu Aminu daga jihar Zamfara ne suka zama zakaru a gasar karatun Alƙur'ani karo na 36 da aka kammala kwanan nan.

Hukumar dillancin labarai ta Najeriya (NAN) ta rahoto cewa mutanen biyu sun lashe gasar ne a rukunin yan Izu 60 a ɓangaren maza da kuma na ɓangaren mata.

Gasar ta kwashe mako ɗaya ana gudanar da ita kuma gidauniyar gasar karatun littafi mai tsarki ta Najeriya da Cibiyar ilimin addinin musulunci ta Jami'ar Usman Danfodiyo dake Sokoto ne suka ɗauki nauyi.

Kara karanta wannan

Dan sanda ya halaka rayuka 2 yayin da ya yi kokarin tserewa daga masu kama shi a Bauchi

Gasar karatun Alkur'ani Mai Girma
Zamfara da Borno sun zama sakaru, sun lashe gasar karatun Alkur'ani Izu 60 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Hakanan kuma gasar wacce aka karkare ranar Asabar a Bauchi ta gudana ne bisa tallafi da haɗin kan gwamnatin jihar Bauchi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Yan gasa 328 ne suka fafata daga jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja a rukunai shida da aka karƙasa gasar karatun.

Rukunan sun haɗa da na gasar karatu na mahaddata Izu 60 da Tajwidi da Tafsiri, .ahaddata Izu 60 na Alkur'ani da Tajwidi kaɗai, sai kuma ɓangaren mahaddata Izu 40 na littafin Allah mai tsarki.

Sauran sune karatun Izu 40 da Tajwidi, haddar izu 10 na Alƙur'ani mai girma da kuma haddar Izu biyu na farko a cikin Littafi mai girma.

Kyaututtukan da aka ba waɗan da suka samu nasara

Mutun biyu da suka zama zakaru sun samu kyauyar Chaki na Naira Miliyan N3m daga Gwamna Bala Muhammed Na Bauchi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun kashe babban Basarake a kan hanyar zuwa gaida mara lafiya

Musa Ahmed da Fatima Tijjani daga jihar Borno sun koma gida da farin cikin Miliyan N2m bisa kwazon da suka nuna a gasar Izu 60 da fassara wasu ayoyin Alƙur'ani.

Da yake jawabi shugaban jami'ar Ɗanfodio kuma shugaban gidauniyar da ta shirya gasar, Farfesa Lawal Bilbis, ya roƙi yan takarar da suka fafata su yi amfani karin gogewar da suka samu a gasar.

NAN ta rahoto cewa mai Alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Sa'ad Abubakar, Sarkin Bauchi, Jama'are, Dass, Katagum, Misau da Ningi, su halarci taron ba da kyaututtukan.

A wani labarin kuma Yadda wani ɗan kasuwa ya halaka yan bindigan da suka yi garkuwa d shi, ya dawo gida lafiya

Wani ɗan kasuwa a Ondo ya yi jarumta a sansanin yan bindiga ya kashe mutum biyu yayin da bacci ya ɗauke su.

Bayanai sun nuna cewa mutumin ya yi kamar yana bacci mai nauyi, suma suka kwanta sai ya tashi ya ɗauki makamansu.

Kara karanta wannan

Majalisun tarayya zasu ɗaukaka kara kan hukuncin goge dokar zaɓe ta Buhari, sun ɗauki wasu matakai

Asali: Legit.ng

Online view pixel