Bauchi: Miji Da Mata Da Wani Sun Mutu Yayin Da Tanka Man Fetur Ta Yi Taho Mu Gamu Da Motarsu, Wasu Sun Jikkata

Bauchi: Miji Da Mata Da Wani Sun Mutu Yayin Da Tanka Man Fetur Ta Yi Taho Mu Gamu Da Motarsu, Wasu Sun Jikkata

  • Akalla mutane 3 ciki har da mata da miji sun rasa rayukansu yayin da sauran mutane 8 suka raunana sakamakon hadarin motan da ya auku a wurare daban-daban cikin Jihar Bauchi
  • Kamar yadda hukumar kiyaye hadurran kan titi ta bayyana, lamarin ya auku ne a yankin Bara a ranar Alhamis, kuma hadarin farko ya faru ne da misalin karfe 9:30 na safe
  • Mata da mijin sun rasu ne suna hanyar zuwa kauyensu da ke Jihar Adamawa yayin da suke shirin halartar wani daurin aure, kuma sun mutu sun bar yara 4

Bauchi - Akalla mutane 3, ciki har da mata da miji, sun rasa rayukansu, yayin da mutane 8 suka raunana sakamakon wasu hadurran motoci da aka tafka a wurare daban-daban cikin Jihar Bauchi, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dan sanda ya halaka rayuka 2 yayin da ya yi kokarin tserewa daga masu kama shi a Bauchi

Kamar yadda rahoton da hukumar kula da hadurran motocin kan titi, FRSC yankin Bara da ke Jihar Bauchi ya nuna na ranar Juma’a, hadarin farko ya auku ne ranar Alhamis, 24 ga watan Maris da misalin karfe 9:30 na safe.

Bauchi: Miji Da Mata Da Wani Sun Mutu Yayin Da Tanka Man Fetur Ta Yi Taho Mu Gamu Da Motarsu, Wasu Sun Jikkata.
Miji Da Mata Sun Rasu Sakamakon Hadarin Mota Da Tankar Man Fetur a Bauchi. Hoto: The Nation.
Asali: UGC

Mata da mijin suna hanyarsu ta zuwa daurin aure ne

Hadarin ya faru ne a kauyen Kaji, babu nisa da iyakar Jihar Bauchi da Gombe da ke kan babban titi.

Ababen hawa biyu ne suka gwabza karo, tankar man fetur wacce wani Adamu Garba ya tuko, da kuma wata mota kirar Toyota Corolla mai lambar rijista RBC 719 DN, wacce wani Babangida Yaro ya tuko.

The Nation ta tattaro bayanai akan cewa Babangida Yaro ma’aikacin kamfanin wutar lantarkin Jos ne, JEDC, kuma yana kusa da ofishin Yelwa da ke Bauchi ya rasa ransa tare da matarsa.

Kara karanta wannan

Da dumi: Jihar Kaduna ta sake daukar dumi yayin da yan bindiga suka kashe mutum 50, sun yi awon gaba da wasu

Miji da matar da suka mutu sun bar yara 4

Babangida dan shekara 50 da doriya ne, kuma yana hanyar tafiya kauyensu da ke Adamawa don halartar wani daurin aure ne ya gamu da ajalinsa.

Sun mutu sun bar yara hudu.

Dayan hadarin, wanda ya ritsa da wata mota kirar Toyota Sienna ya yi ajalin mutum daya, wurin kauyen Gumeru da ke kan babban titin Bauchi zuwa Kano.

Hadarin ya ritsa da wata motar gida, mai lambar rijista: ABC 755 TS, wacce Salman Tanko ya tuko.

Hadarin ya ritsa da mutane 7 ne kamar yadda aka samu rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel