Budurwa ta arce da N140,000 da na'urar POS kwana daya da daukarta aiki

Budurwa ta arce da N140,000 da na'urar POS kwana daya da daukarta aiki

  • Wani dan Najeriya mai suna @Letter_to_Jack yana neman wata budurwa wacce ta yi awon gaba da kudi N140,000
  • Budurwar ta tafi da kudin maigidanta da na'urar POS a ranar farko da ta fara aiki da mutumin a Legas
  • @Letter_to_Jack ya daura wannan a shafinsa na Facebook inda yake rokon duk wanda ya santa ya fada masa

Wani dan Najeriya mai suna @Letter_to_Jack a Tuwita ranar Laraba, 23 ga Maris, ya bayyana wata budurwa mai suna Ashiru Dupe Adedayo, wacce ta gudu da kudin maigidanta.

A cewarsa, ranar farko da fara aiki, an baiwa Dupe N100,000 da na'urar POS mai dauke da 40,000 ciki.

Budurwa ta arce da N140,000 da na'urar POS kwana daya da daukarta aiki
Budurwa ta arce da N140,000 da na'urar POS kwana daya da daukarta aiki Hoto: @Letter_to_Jack, @hmbventure
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lambar da zaka kira idan ka ganta

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun halaka dan kasuwa, sun sace matarsa da yaransa

@Letter_to_Jack ya saki hotunansa da bayanan da ya rubuta a takardar neman aikinta kuma an gano karya ne.

Shagon POS na unguwar Fagba, Iju Bus stop, karamar hukumar Ifako Ijaiye.

Ya ajiye lambar kira +2348147724954.

Tsokacin yan Najeriya

Helena Robert tace:

"Irin waɗannan ne suke hana a taimakawa ƴan uwansu masu neman ɗaukin rayuwa
ALLAH ka tsare mu butulci ga masu nufinmu da alheri."

Najmuddeen Ibraheem Jungudo:

Ta gwada mishi bariki ne se yayita nemanta har yamutu

Mubarak Saeed Bakori:

Ana iya shege a kasata nigeria, tayi wuf da shi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel