Abubuwa 5 da Atiku yace zai tabbatar ya yi idan yan Najeriya suka zabeshi

Abubuwa 5 da Atiku yace zai tabbatar ya yi idan yan Najeriya suka zabeshi

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, ya bayyana matakinsa nasa ne a babban dakin taron International Conference Centre da ke Abuja.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci ayyanawar ta Atiku sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Muhammad Namadi Sambo; Gwamnan jihar Adamawa Umaru Fintiri; Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, Cif Tom Ikimi da dai sauran jiga-jigan PDP.

Sauran magoya bayan nasa da suka halarci bikin da ke ci gaba da gudana har yanzu sun hada da Sanata Dino Melaye, Ambasada Roland Omowa da Josephine Anenih.

Atiku Abubakar
Abubuwa 5 da Atiku yace zai tabbatar ya yi idan yan Najeriya suka zabeshi Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya ayyana kudurinsa na gaje kujerar Buhari a zaben 2023

A jawabin da ya gabatar a taron ayyana niyar, Atiku ya bayyana jerin abubuwa biyar da zai mayar da hankali kansu idan yan Najeriya suka zabesa ya zama shugaban kasa.

Yace:

"Karkashin mulki na, zan mayar da hankali kan wasu abubuwa biyar: Hadin kan Najeriya, Tsaro, Tattalin arziki, Ilimi, da kuma baiwa jihohi iko kan dukiyarsu."

Tambuwal: Zamu zauna da Atiku domin duba yuwuwar sulhu wajen tsayar da ɗan takara a 2023

Ɗan takarar shugaban ƙasa kuma gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya ce zai tattauna da Atiku Abubakar domin duba yuwuwar fitar da ɗan takarar PDP ta hanyar sulhu.

Gwamna Tambuwal ya faɗi haka ne yayin da yake hira a cikin wani shiri na kafar watsa labarai, Channels TV ranar Talata.

Wannan cigaban na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Tambuwal, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, sun amince da fitar da mutum ɗaya a cikinsu.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Gwamna Tambuwal ya gana da IBB da Abdulsalami, ya bayyana shirin ‘yan takarar PDP

Da yake tsokaci ranar Talata, gwamnan Sokoton ya ce yana da nagartar da ake bukata wajen lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel