Hisbah Ta Yi Ram da Maza 44 Da Mata 54 Suna Tsaka Da Aikata Masha'a a Jihar Jigawa

Hisbah Ta Yi Ram da Maza 44 Da Mata 54 Suna Tsaka Da Aikata Masha'a a Jihar Jigawa

  • Rundunar Hisbah, reshen Jihar Jigawa, ta kama mutane 99 a karamar hukumar Kazaure da kuma Dutse cikin jihar suna tsaka da aikata alfasha
  • Kwamandan rundunar, Malam Ibrahim Dahiru ya tabbatar da aukuwar lamarin a Dutse ranar Talata, 17 ga watan Maris na shekarar 2022
  • Rundunar ta bayyana cewa cikin wadanda aka kama akwai maza 44 da mata 54, kuma an yi ram da su yayin da suke tsaka da lalata da sauran ayyukan masha’a

Jigawa - Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa ta samu nasarar kama mutane 99 a karamar hukumar Kazaure da Dutse da ke cikin jihar bisa zargin su da aikata masha’a, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kwamandan rundunar, Malam Ibrahim Dahiru ya tabbatar wa da NAN hakan a Dutse, babban birnin jihar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 8 da Hukumar Kwastam ta hana fitar da su zuwa kasashen waje

Hisbah Ta Yi Ram Maza 44 Da Mata 54 Suna Tsaka Da Aikata Masha'a a Jihar Jigawa
Hisbah Ta Kama Maza 44 Da Mata 54 Suna Tsaka Da Aikata Masha'a a Jihar Jigawa. Hoto: Nigerian Tribune

Dahiru ya ce wadanda ake zargin, akwai mata 54 da maza 44 a cikin su kuma a ranar 16 ga watan Maris da kuma 17 ne rundunar ta kama su a samamen da suka kai daban-daban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kama su suna lalata da junayen su

Ya bayyana yadda aka kama mutane 91 cikin masu laifin, wanda cikin su mata 49 da maza 42 a ranar 16 ga watan Maris yayin da suka kai samame kauyen Gada da ke Kazaure.

A cewarsa, ana zargin wadanda aka kama da yin lalata da junayen su tare da yin sauran ayyukan masha’a.

Sai dai Dahiru ya ce ba a kama 21 daga cikin mazan tare da mata ba.

Dahiru ya yaba wa ‘yan sanda da mazauna yankin akan ba su hadin kai

Kwamandan ya ce an kama sauran mutane 8 din da ake zargi, ciki akwai mata 5 da maza 3 a ranar 17 ga watan Maris a garin Dutse.

Kara karanta wannan

Zamfara: Mun dauki masu gadin al’umma 4200 don yaki da ‘yan ta'adda

Ya kara da cewa sun kwace kwalabe 8 na giya yayin da suka kai samamen.

Ya ce Hisbah za ta ci gaba da kai samame duk wani lungu da sakon da aka san ana aiwatar da miyagun al’amura a fadin jihar, rahoton Nigerian Trubune.

Dahiru ya kara da yaba wa ‘yan sanda da mazauna yankin akan kokarin su na bayar da goyon baya da kuma hadin kai ga rundunar wanda hakan ya taimaka mata wurin yin ayyukan ta da kyau.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel