Hotuna 5 na wankan biloniya Otedola da ke nuna tsabar aji da tsarinsa

Hotuna 5 na wankan biloniya Otedola da ke nuna tsabar aji da tsarinsa

  • Fitaccen dan kasuwan nan, Femi Otedola ba mutum bane mai sanya sutturu masu tsada a duk lokacin da zai bayyana ga jama'a
  • Bayan dubi ga hotunan biloniyan a shafinsa na Instagram na nuna yadda yake son sanya sutturu masu sauki, tsafta kuma masu aji
  • Legit.ng ta tattara wasu saukakan hotunan Otedola da ke nuna wasu daga cikin shigarsa a biki, mahimman taruka da sauransu

Shahararren dan kasuwan nan na Najeriya, Femi Otedola, yana da isashshen kudin da zai iya siyan tsadaddu da kasaitattun tufafi, amma hakan baya daga cikin tsarinsa.

Biloniyan yafi jin dadin yin abubuwa masu kayatarwa, kuma masu aji, hakan zai sa mutum tunanin ko dai diyarsa, Temi Otedola ta na koyi da shi ne.

Hotuna 5 na wankan biloniya Otedola da ke nuna tsabar aji da tsarinsa
Hotuna 5 na wankan biloniya Otedola da ke nuna tsabar aji da tsarinsa. Hoto daga @femiotedola
Asali: Instagram

A duk lokacin da ya bayyana a taron jama'a ko wani mahimmin taro, za ka ga hamshakin dan kasuwan a sutturun da suka dace da wurin da yake.

Kara karanta wannan

Daukar fansa: Fusatattun matasa sun far wa matafiya a wani yankin Kaduna

Legit.ng ta tattara wasu daga cikin hotunan da ke nuna hadaddun sutturun Otedola.

1. Kaunar da Otedola ke wa fararen kaftani

Bayyanannun hotuna a shafin Otedola na Instagram na nuna yadda yake matukar kaunar kaftani.

Sai dai, biloniyan ya fi maida hankali wajen saka kayatattun hulunan aso-oke da suka fi dacewa da fararen kaftani.

2. Otedola da kwat da wando mai riguna biyu tare

Yayin halartar taron da ya shafi kasuwanci ko bayyana a mahimman wurare, dan kasuwan yafi son sanya kwat mai riguna biyu. Otedola ya zabi ta'ammuli da kaloli irinsu; ruwan toka, ruwan bula mai duhu da baki a wasu lokutan.

3. Kaunar da Otedola ke jaket

Duba da yanda dan kasuwar ke yawan zama a babban birnin Amuruka, ba abun mamaki bane idan ance jerin tufafinsa sun cika da tufa irin yanayin na garin Amuruka.

Kara karanta wannan

Zamfara: Mun dauki masu gadin al’umma 4200 don yaki da ‘yan ta'adda

Dan kasuwan yana da wani irin tsarin sanya tufafi da suke matukar amsar jikinsa, tsakanin rigar da ake dorawa akan tufa, wanduna kirar jeans da tsadaddun takalma kirar Oxford. Mutum ne izza!

4. Waye ya ce yara kadai ke sanya Tracksuit?

Wata kila dai abu ne na wani lokaci. Sai dai, a lokacin kullen da aka yi na cutar Korona, an ga Otedola na daukar wankan riga da wandon sanyi masu kayatarwa iri-iri da suka dace da takalma Sneakers.

5. Bayyana kafafu da Otedola yake yawan yi

Otedola ba ya damuwa da bayyana kafafunsa, hotunan na nuna cewa ya san wankan da suka dace da yanayin wurin.

Kuma yana daukar wankan ne daidai da irin wurin da zai halarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel