Magana ta kare: Minista ya amince a karbe dukiya da kadororin Abba Kyari da mutanensa

Magana ta kare: Minista ya amince a karbe dukiya da kadororin Abba Kyari da mutanensa

  • Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami SAN ya amince da bukatar da NDLEA ta kawo masa
  • Hukumar NDLEA ta nemi gwamnatin tarayya ta lamunce mata ta rike dukiyarsu DCP Abba Kyari
  • NDLEA ta na zargin Kyari da wasu jami’an ‘yan sanda sun yi kudi ne da harkar safarar kwayoyi

Abuja - Babban lauyan gwamnatin tarayya, kuma Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami ya amince da rokon da NDLEA ta gabatar a kan su Abba Kyari.

Jaridar Punch ta ce Abubakar Malami SAN ya yarda hukumar NDLEA mai yaki da safarar miyagun kwayoyi ta karbe dukiyar Abba Kyari da mutanensa.

A halin yanzu hukumar NDLEA ta na shari’a da DCP Abba Kyari da wasu jami’an ‘yan sanda.

Rahoton ya ce rokon da hukumar NDLEA ta ke yi ya je gaban Mai girma Ministan shari’a a makon da ya gabata, kuma Ministan ya amince da wannan bukatar.

Kara karanta wannan

Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari

Za su rasa arzikinsu?

Hakan na nufin tsohon shugaban rundunar IRT na ‘yan sanda da sauran wadanda ake tuhumarsu da laifi tare za su iya rasa kadarorinsu da kudinsu da ke banki.

Ministan shari'a
Ministan shari'a, Abubakar Malami Hoto: Twitter
Asali: Twitter

Haka zalika jami’an ‘yan sandan su na iya asarar motoci, abubuwan hawa, gidaje, otel, gine-gine da sauran kaya masu matukar daraja kamar agogo da sauransu.

Haka kuma wani labari da muka samu dazu ya tabbatar da cewa AGF ya yi na’am da rokon NDLEA.

"Minista ya sa hannu"

Majiyar da ta fito daga ma’aikatar shari’a ta kasa, ta ce bukatar hukumar ta NDLEA na karbe dukiyar da su Kyari suka mallaka ta samu amincewar Malami SAN.

Ana zargin DCP Kyari, Ubuah da sauran ‘yan sandan su na da hannu wajen safarar kwayoyi.

Kara karanta wannan

Abba Kyari: Yadda NDLEA Ta Taimakawa Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi Wurin Shigo Da Hodar Iblis Najeriya

“Tun da aka amince da rokon, hukumar za ta iya karbe masu gine-gine, kudi, dukiyar da ke bankuna, abubuwan hawa, hannun jari da duk wani abu mai daraja.”

- Majiyar ma'aikatar tarayya

Majiyar ta ce makasudin hakan shi ne a tabbatar da cewa wadanda ake tuhuma ba su amfana da wadannan kudi da ake zargin daga cinikin kwayoyi aka same su ba.

N4.2bn su na kwance a akawun

A makon da ya wuce, an fitar da rahoto cewa an samu sama da Naira biliyan 4 a asusun DCP Abba Kyari da tsohon mataimakinsa a IRT, ACP Sunday Ubua a bankuna.

Binciken da jami’an NDLEA su ka gudanar ya nuna cewa N4.2bn ya shiga asusun ‘yan sandan NDLEA. Ana zargin daga wani cinikin Tramadol aka samu wannan kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel