Abba Kyari: Yadda NDLEA Ta Taimakawa Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi Wurin Shigo Da Hodar Iblis Najeriya

Abba Kyari: Yadda NDLEA Ta Taimakawa Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi Wurin Shigo Da Hodar Iblis Najeriya

  • Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar ya zargi jami’an hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA da taimaka wa masu safarar hodar iblis zuwa Najeriya
  • Kyari da ake shari’a da shi a babbar kotun Abuja bisa zargin sa da shiga cikin wani ciniki na hodar iblis, ya ce jami’an NDLEA ne suka hada masa sharri don su bata masa suna
  • Mutane sun sa ido akan shugaban rundunar binciken sirrin, IRT wanda ya yi fice wurin fallasa masu laifuka daban-daban tun bayan gwamnatin Amurka ta zarge shi da shiga wata damfarar yanar gizo

Abuja - Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda wanda aka dakatar ya zargi jami’an hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA da yi wa masu safarar hodar iblis rufa-rufa wurin shigar da ita Najeriya, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bacin zuciya: Kotu ta yankewa malamin addini hukuncin kisa bayan ya kashe amininsa

Kyari, wanda yanzu haka ake shari’ar sa a babbar kotun Abuja akan zarginsa da shiga wani rikicin hodar iblis ya ce wasu jami’an NDLEA marasa gaskiya ne suka hada masa sharrin don ya nemi a biya wani mai taimaka wa jami’an binciken sirri wurin kama masu laifi.

Abba Kyari: Yadda NDLEA Ta Taimaka Wa Masu Safarar Miyagun Kwayoyi Wurin Shigo Da Hodar Iblis
Abba Kyari: Yadda NDLEA Ta Taimaka Wa Masu Safarar Miyagun Kwayoyi Wurin Shigo Da Hodar Iblis. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idon jama’a yana kan Kyari wanda a baya shi ne shugaban rundunar binciken sirri, IRT, wanda ya dade yana fallasa masu laifuka, tun bayan gwamnatin Amurka a zarge shi da shiga wata damfarar yanar gizo ta miliyoyin daloli.

Tun farko gwamnatin Amurka ta zargi Kyari da damfarar yanar gizo

Gwamnatin Amurka ta nemi Kyari ido rufe bisa zargin sa da taimaka wa wani fitacce a Instagram, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Huspuppi wurin damfarar miliyoyin daloli.

Yayin da Huspuppi ya ke jiran hukunci, a babbar kotun California, kamar yadda Premium Times ta ruwaito, hukumar NDLEA ta rike Kyari inda take zarginsa da wani laifin na daban.

Kara karanta wannan

Labarin cikin Hotuna: Mai Mala Buni yayi takakkiya zuwa Landan don ganin Shugaba Buhari

A ranar 7 ga watan Maris, Kyari da wasu jami’an ‘yan sanda suka gurfana gaban alkalin babbar kotun Abuja inda ake zargin su da safarar hodar iblis.

Chibuna Umeibe da Emeka Ezenwanne, wadanda duk ba ‘yan sanda bane sun amsa laifukan su na safarar hodar iblis mai nauyin kilogram 21.35.

Sai dai Kyari da sauran ‘yan sanda 4 suka musanta duk laifuka takwas da ake zargin su da aikatawa.

Bayan kama Kyari a ranar 12 ga watan Fabrairu har zuwa makon da ya gabata, ya maka karar NDLEA akan shiga hakkin sa na dan adam.

Ya bukaci N500m a matsayin diyyar shiga hakkinsa na hana shi yawo da sauran su, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Batun taimaka wa masu safarar miyagun kwayoyi

A wata takardar kotu wacce wani Muhammad Nur Usman, wanda ya ce shi kanin Kyari ne ya gabatar, ya sanar da kotu cewa jami’an NDLEA da kan su suke taimaka wa wani mai safarar miyagun kwayoyi kuma su raka shi gida tun daga filin jirgin sama, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: NSCDC Ta Kama Wani Mutum Da Katin Waya 22 Da Katin ATM 14

Yayin karin bayani akan tafiyar ta shi wacce ta kai ga hukumar ta kama shi, Kyari cewa ya yi:

“A ranar da lamarin zai faru, wanda ake zargin yana safarar miyagun kwayoyin kamar yadda ya saba daga Ethiopia zuwa filin jirgin Enugu, jami’in NDLEA din ya duba shi sannan jami’an FIB-IRT suka kama shi bayan an ba su bayanan sirri.
“Kafin mai bayar da bayanin ya amince yayi aiki da jami’an FIB-IRT din, sai da suka yi yarjejeniya akan cewa zasu ba shi diyya idan ya bayar da bayanin.
“Bayan jami’an FIB-IRT sun lura da cewa jami’an NDLEA ne suke duba kayan wanda ake zargin yana safarar miyagun kwayoyin, sun yi gaggawar mika shi ga hukumar NDLEA sannan suka kai karar jami’an su da ke da hannu a lamarin.”

Ya ci gaba da bayyana cewa maimakon NDLEA ta yi abinda ya da ce ta kuma hukunta jami’an ta da suka shiga lamarin, sai ta tasa wanda ya kai labarin gaba sannan ta ki biyansa diyya.

Kara karanta wannan

Rashin wuta ya jawo an koma dogara da Janaretoci har a fadar Shugaban kasar Najeriya

Ya ce a lokacin ne aka sanar da DCP Abba Kyari lamarin da ya faru, kasancewar jami’in NDLEA da ya bayar da bayanan sirri abokin shi ne, wanda ya yanke shawarar shiga lamarin don ya sa baki a biya wanda ya kai bayanin diyya.

A cewarsa, jami’in NDLEA din da ya ki biyan wanda ya kai bayanin sirrin diyya daga nan ya shirya wa DCP Kyari sharri akan cewa ya yi yunkurin ba shi rashawa, ba tare da kawo kwakwkwarar hujja ba.

Jami’an ‘yan sanda sun yi gaggawar kama Kyari a ranar 12 ga watan Fabrairun 2022 bisa zargin da aka yi masa inda suka mika shi ga NDLEA a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel