Farashin lantarki ya tashi bayan Gwamnati tayi wuf, ta dakatar da tallafin wuta

Farashin lantarki ya tashi bayan Gwamnati tayi wuf, ta dakatar da tallafin wuta

  • Nigerian Electricity Regulatory Commission ta ce farashin lantarki ya tashi daga watan Fubrairu
  • Shugaban hukumar NERC, Sanusi Garba ya ce hakan ya biyo bayan janye tallafin wutar lantarki
  • An zo lokacin da gwamnatin tarayya ta gaji haka nan, ta daina biyan tallafi domin a samu rahusa

Abuja - Hukumar Nigerian Electricity Regulatory Commission mai kula da harkar wutar lantarki a Najeriya ta ce gwamnatin tarayya ta janye tallafin wuta.

Punch ta rahoto hukumar NERC a ranar Laraba ta na cewa tallafin shan wutan da ya ci wa gwamnatin tarayya N600bn ya zo karshe a halin yanzu.

NERC ta bada sanarwar kara farashin shan wutar lantarki a Fubrairun wannan shekara ta 2022. An dauki wannan mataki ba tare da wani bata lokaci ba.

Hakan na zuwa ne a lokacin da kamfanonin da ke samar da wuta su ka soki aikin NBET, suka ce kamfanin ya gagara yin abin da ya dace na biyansu kudinsu.

Kara karanta wannan

Rashin wuta ya jawo an koma dogara da Janaretoci har a fadar Shugaban kasar Najeriya

Sanusi Garba ya zanta da 'yan jarida

Kamar yadda aka kawo rahoton a Nairaland, shugaban hukumar NERC na kasa, Sanusi Garba ya bada wannan sanarwa ne da ya zanta da manema labarai.

Garba ya ce aikin NERC shi ne tsaida farashin da masu shan wuta za su biya. Hakan ya na nufin hukumar ta na shiga tsakanin kamfanonin wuta da jama’a.

Lantarki
Kayan wutar lantarki Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

“A shekaru hudu zuwa biyar da suka wuce, an rage adadin tallafin da ake badawa, saboda ba zai yiwu a rika saida wutar lantarki da kame-kame ba.”
“Ba zai yiwu a ce ‘yan kasuwa ba za su maida kudinsu ba har sai gwamnati ta tsoma kanta.”
“Saboda haka kamar yadda Ministar tattalin arziki ta bada sanarwa, an janye tallafin wutar lantarki. Akwai lokacin da ake biyan N600bn a shekara.”

Kara karanta wannan

Ido zai raina fata yayin da Shugaban kasa ya ce a hukunta wanda suka jawo wahalar fetur

“Kudin ya zo ya yi ta yin kasa sannu a hankali, har ya kai N30bn a shekarar nan.” - Sanusi Garba.

Farashi zai rika canzawa

A ranar 1 ga watan Fubrairun 2022 aka samu sauyin farashi a kasar nan. NERC ta ce duk bayan watanni shida ya kamata farashin wuta ya canza a kasuwa.

Farashin yana canzawa ne sakamakon canjin kudin kasar waje da tsadar kaya a kasuwa.

Babu fetur...babu wuta

Ku na sane da cewa a makon nan an yi ta samun tangarda a tashoshin Najeriya har Ministann harkar lantarki, Abubakar Aliyu ya kira wani taron gaggawa.

Injiniya Abubakar Aliyu ya shaida cewa masu fasa bututun mai a Neja-Delta ne suka taba layin gas da na’urorin samar da wutan kasar nan suke amfani da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel