Gaskiya ta bayyana a zargin da ake yi wa tsohon hafsun soja na cin miliyoyi a mulkin Jonathan

Gaskiya ta bayyana a zargin da ake yi wa tsohon hafsun soja na cin miliyoyi a mulkin Jonathan

  • Babban kotun tarayya ta ba EFCC rashin gaskiya a shari’arta da Air Marshal Mohammed Umar (rtd)
  • Hukumar EFCC ta hakikance kan cewa AVM Mohammed Umar ya saci N66m da nufin gyaran gida
  • Alkali ya zartar da hukunci cewa babu abin da ke nuna tsohon sojan ya dauki kudi daga asusun NAF

Abuja - Babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja, ta wanke Air Marshal Mohammed Umar (mai ritaya) daga zargin daukar N66m daga asusun NAF.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Alhamis cewa kotu ba ta samu Air Marshal Mohammed Umar da laifin hukumar EFCC da ke zargin sa da aikatawa ba.

A ranar 17 ga watan Maris 2022, Alkali Nnamdi Dimgba ya ce babu hujjar da ke nuna tsohon sojan ya yi amfani da kudin gidan soja, ya gyara gidansa a Abuja.

Kara karanta wannan

EFCC ta yi nasara, kotu ta raba tsohon babban soja da matarsa da dukiyarsu har abada

Hukumar EFCC ta na zargin Umar ya saci N66m daga wani akawun na aikin sojojin saman Najeriya a banki zuwa, da nufin ya gyara gidansa a Abuja.

Lauyoyin EFCC sun ce gidan ya na nan a layin Deng Xiao Ping Street, gaba da titin Mahathir Mohammed Street, Asokoro Extension a babban birnin tarayya.

Jaridar tace lauyoyin EFCC sun kafa hujja da cewa wannan danyen aiki da AVM Umar ya yi, ya saba sashe na 15(2) na dokar safarar kudi na shekarar 2011.

Tsohon hafsun soja
Air Marshal Mohammed Umar Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Alkali bai gamsu ba

Mai shari’a Nnamdi Dimgba ya saurari korafin hukumar EFCC, ya ce ba su iya gamsar da kotu da isassun hujjojin da za su sa a kama wanda ake zargi da laifi ba.

Nnamdi Dimgba ya ce akwai bukatar a tabbatar da cewa AVM din ya aikata wannan laifi karara.

Kara karanta wannan

Gobara ta kona wurin da hukumar EFCC ta ke tara hujjar binciken marasa gaskiya

“Na samu wanda ake tuhuma bai aikata laifi daya tilo da ake zarginsa da shi ba, a dalilin haka, na wanke shi, na yi watsi da karar.” - Nnamdi Dimgba

Zai dawo da N57m

Amma jaridar Pulse ta ce Alkalin kotun tarayyar ya bukaci Umar ya dawo da N57m da aka turo masa, ya maidawa gwamnati ko a karbe gidan na sa da ke Asokoro.

Tsohon hafsun sojan ya karbi N57m ne da sunan za ayi gyaran gidansa. Alkalin ya ce dole ya dawo da kudin nan da kwanaki bakwai domin bai dace ya ci su ba.

Hushpuppi ya yi ta'asa a daure?

An ji cewa babban lauyan gwamnatin kasar Amurka ya ce maganar a ce Ramon Azeez ya damfari Bayin Allah yayin da yake zaman kaso ba ta da tushe da makama.

Lauyoyin da ke kare Hushpuppi sun karyata wadannan labarai. Haka wani masani kuma malamin jami’a ya ce labarin bogi ne da ‘yan damfara suka kirkiro.

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Alkalin kotun Abuja ya shiga jerin wadanda ake tuhuma da rashin da'a

Asali: Legit.ng

Online view pixel