Neja: Ƴan Bindiga Sun Ji Ba Daɗi A Hannun Jami'an Tsaro, Fiye Da 100 Sun Baƙunci Lahira

Neja: Ƴan Bindiga Sun Ji Ba Daɗi A Hannun Jami'an Tsaro, Fiye Da 100 Sun Baƙunci Lahira

  • Dakarun sojojin Najeriya, yan sandan Najeriya da yan sakai a jihar Neja sun yi nasarar dakile wata hari da yan bindiga suka kawo Bangi
  • Yayin artabun da suka yi, jami'an tsaron sun yi ci galaba a kan yan bindigan inda suka halaka fiye da 100 sannan suka kwato babura da dama
  • Emmanuel Umar, kwamshinan kananan hukumomi, masarautu da tsaro na jihar Neja ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce yan bindigan sun taho ne daga Nasko

Neja - Jami'an tsaro na hadin gwiwa da suka hada da sojoji, yan sanda da yan sakai da ake kira vigilante a ranar Laraba da yamma sun dakile wata harin da yan bindiga suka so kai wa a Bangi, hedkwatar karamar hukumar Mariga, Jihar Neja.

Mazauna garin sun bayyana cewa yan bindigan da suka nufo garin sun yi yunkurin kutsa wa hedkwatar ne misalin karfe 6 na yamma amma hadakar jami'an tsaron suka dakile harin, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yan sanda da Sojoji sun yi wa yan bindiga rubdugu a Abuja, sun ceto mutum ɗaya

Neja: Ƴan Bindiga Sun Ji Ba Daɗi Hannun Jami'an Tsaro, Fiye Da 100 Sun Baƙunci Lahira
Neja: Ƴan Bindiga Sun Ji Ba Daɗi Hannun Jami'an Tsaro, Sun Aika Da Fiye Da 100 Barzahu. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Kwamishina ya tabbatar da lamarin, ya ce daga garin Nasko 'yan binigan suka taho

Daily Trust ta rahoto cewa Kwamishinan kananan hukumomi, masarautu da tsaro na jihar, Emmanuel Umar, ya ce an kashe fiye da yan bindiga 100 yayin harin an kuma kwato babura masu yawa.

Ya ce yan bindigan sun taho ne daga Nasko inda suka halaka jami'in dan sanda mai mukamin DPO da wasu jami'an tsaro a ranar Talata domin su kaddamar da wata harin a Bangi, karamar hukumar Mariga na jihar a wannan yankin.

Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane, sun ƙona gidaje masu yawa

A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla fararen hula uku ne suka riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai hari a kauye da ke karamar hukumar Chibok a Jihar Borno da yammacin ranar Jumma'a.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bindige DPO da wasu jami'ai 6 har lahira a wani mummunan artabu a Neja

Kungiyar yan ta'addan sun afka kauyen Kautikari da ke kusa da gari Chibok misalin karfe 4 na yamma, suna harbe-harbe ba kakkautawa kuma suka kona gidaje da dama a cewar majiyoyi na tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar majiyar, maharan sun iso ne a cikin motocci guda biyar dauke da bindiga mai harbo jiragen yaki kuma suka shigo cikin sauki ba tare da an nemi taka musu birki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel