Rashin da'a da karya: Gwamnatin Buhari ta shiga damuwa kan yadda ake amfani da Tik-Tok

Rashin da'a da karya: Gwamnatin Buhari ta shiga damuwa kan yadda ake amfani da Tik-Tok

  • Gwamnatin tarayya ta shiga damuwa game da yadda mutane ke amfani da Tik-Tok ta hanyoyin da basu dace ba
  • Wannan na zuwa ne yayin da ma'aikatar sadarwa ta zauna da wasu wakilan kamfanin na Tik-Tok a Abuja
  • Gwamnati ta bayyana bukatar dakatar da wasu mutane da ke yada abubuwan da basu dace a kafar ta sada zumunta

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta tabo batutuwa da dama da suka shafi tsaro, biyan haraji da kuma tsaftar abubuwan da ake yadawa a kafar yada bidiyo ta Tik Tok, rahoton Daily Trust.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamnai, Isa Ali Pantami, wanda ya karbi bakuncin tawaga daga TIkTok a Abuja ya bayyana hakan a jiya Laraba.

Dr Pantami ya magantu kan batun Tik-Tok
Rashin da'a da karya: Gwamnatin Buhari ta shiga damuwa kan amfani da Tik-Tok | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ya jaddada bukatar bin gaskiya, dokoki da ka'idoji wajen amfani da kafar don tabbatar da ingantaccen sararin yanar gizo ba tare da keta doka ba da kuma dakile masu tallata labaran karya.

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai Ya Umurci Duk Masu Riƙe Da Mukaman Siyasa Da Ma'aikatan Gwamnati Masu Son Takara Su Ajiye Aiki

Pantami wanda Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), Kashifu Inuwa Abdullahi ya wakilta, ya ce kamata ya yi a samu sakamako ga duk wanda ke amfani da kafar ta sada zumunta wajen aikata laifi.

Ya ce sharuddan da Twitter ya amince da su kafin gwamnati ta dage dakatarwar da ta kakaba masa za a yi amfani dasu kan sauran kafafen sada zumunta da suka hada da TikTok.

Jaridar Tribune ta rahoto Inuwa na cewa:

“A Najeriya, mutane suna amfani da TikTok don abubuwa da yawa; wasu suna amfani da shi don inganta ayyukan tsafi da tashin hankali a cikin gidaje yayin da wasu ke amfani da shi don yada kiyayya; Don haka, ba za mu iya bari mutane su ci gaba da fitar da abubuwan da ba su dace ba ba tare da tantancewa/tabbatar da sun dace ba."

Kara karanta wannan

2023: El'rufai ya umurci kwamishina ya ajiye aiki bisa saboda sha'awar kujerar gwamna

Rikici: Mata ta kai karar TikTok saboda samun matsalar kwakwalwa tsabar kallo a kafar TikTok

A wani labarin, wata mata da ke bitar bidiyo a dandalin bidiyo na TikTok ta kai kara kotu saboda ta haddasa mata wani ciwon kwakwalwa da aka fi sani da Post Traumatic Stress Disorder (PTSD).

Matar, ta ce ta sami ciwon ne saboda aikinta shine duba bidiyon da suka hada da zane-zane, abubuwan tashin hankali da ka'idodin makirci da sauran 'hotuna masu tayar da hankali.'

Candie Frazier, wacce ke zaune a Las Vegas kuma 'yar kwangila ga tushen kamfanin TikTok, ByteDance, ta ce ita da sauran masu bitar galibi suna bata sa'o'i 12 kowace rana suna kallon bidiyoyi masu ban tsoro a kan dandamalin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel