Sheikh Daurawa: Gwamnatin Kano ta ja-kunnen Malaman musulunci da ‘Yan Tik Tok

Sheikh Daurawa: Gwamnatin Kano ta ja-kunnen Malaman musulunci da ‘Yan Tik Tok

  • Wani wa’azi da Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya ambaci tsiraicin mace ya tada kura a jihar Kano
  • Wannan ya sa kwamishinan addini na jihar Kano ya fito yana gargadin malamai da sauran jama’a
  • Muhammad Tahar Adam ya ce malamai su iya bakinsu, kuma ba za a bari a dauki doka a hannu ba

Kano - Biyo bayan wani wa’azi da Aminu Ibrahim Daurawa ya yi a kwanaki, gwamnatin jihar Kano ta fito ta yi magana ta na jan-kunnen malaman jihar.

BBC ta rahoto mai girma kwamishinan addini na jihar Kano, Muhammad Tahar Adam wanda aka fi sani Baba Impossible yana bayyana matsayar gwamnati.

Muhammad Tahar Adam ya bayyana cewa sun saurari wa’azin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi, ya ce akwai bukatar malamai su rika tauna kalamansu.

Kara karanta wannan

Cin mutuncin Daurawa da 'yar Kannywood ta yi: Na yafe wa Nafisa Ishaq, inji Sheikh Daurawa

Dr. Muhammad Adam ya yi kira ga malamai su rika yin wa’azi da kalaman da ba za su rikitar da masu sauraro ba, kuma su guji kalmomi masu kama da batsa.

Martani ga Nafisa Ishaq

Baba Impossible ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kano ta saurari martanin da wata mai suna Nafisa Ishaq tayi a dandalin sada zumunta na Tik Tok.

Biyo bayan kalaman na Nafisa Ishaq sai aka ji Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunnah yana yi mata raddi da cewa mutane irinta su guji yi wa shehunnai rashin kunya.

Gwamnan Kano Ganduje
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje Hoto: @govumarganduje
Asali: Twitter

Asadus-Sunnah wanda mazaunin Kaduna ne ya fitar da faifen bidiyo yana mai barazana ga duk 'marasa kunya' da cewa su na da matasa da za su ladabtar da su.

Gwamnati ta sa baki

Kara karanta wannan

Kano: NSCDC Ta Kama Wani Mutum Da Katin Waya 22 Da Katin ATM 14

Ganin akwai yiwuwar abin ya kai ga barkewar rikici, dole aka nemi gwamnati ta sa bakinta.

Da yake yi wa BBC Hausa jawabi, Kwamishinan addinan na Kano ya ce sun tsaya sauraron duka bangarorin ne, a dalilin haka ne ba su tsoma baki da farko ba.

Rahoton ya ce Tahar ya ba Aminu Daurawa laifi da ya yi maganganun da za su iya kawo rudani.

A cewar kwamishinan, ya kamata Aminu Ibrahim Daurawa ya tsaya a kan abin da Allah da ManzonSa (SAW) suka fada, ya ce ba za su yarda a saba doka ba.

Wace magana Daurawa ya yi?

An ji Aminu Ibrahim Daurawa yana cewa gaba shi ne mafi munin halittar diya mace.Amma wasu mata sun ce malamin ya ci masu mutunci, ya kushe halittarsu.

Amma shehin malamin nan, Dr. Mansur Sokoto ya yi karin bayani kan maganar Daurawa, inda ya nuna cewa ba malamin ne ya fara fadar wannan maganar ba.

Kara karanta wannan

2023: El'rufai ya umurci kwamishina ya ajiye aiki bisa saboda sha'awar kujerar gwamna

Asali: Legit.ng

Online view pixel