Mafarauta a jihar Borno sun kashe katon Zaki a garin Konduga

Mafarauta a jihar Borno sun kashe katon Zaki a garin Konduga

Shugaban Hukumar harkokin gandun daji na ma'aikatar yanayi a jihar Borno, Peter Ayuba, ya tabbatar da kisan Zaki da mafarauta sukayi a karamar hukumar Konduga dake jihar.

Ayuba, ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ranar Talata a Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

Mafarauta a jihar Borno sun kashe katon Zaki a garin Konduga
Mafarauta a jihar Borno sun kashe katon Zaki a garin Konduga Hoto: NAN
Asali: Twitter

Ya ce da yiwuwan Zaki ya shiga jihar ne daga gidan ajiye namomin daji a Kamaru.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Muna samun ire-iren wadannan dabbobi har da giwaye daga daji suna zuwa karamar hukumar Kala-Balge."
"Hakazalika an samu rahoton wasu Kuraye sun kashe wani mutumi a karamar hukumar Kaga."

A bayaninsa, kasancewar mutane sun yi hijira daga garuruwan yasa dabbobi suka fara shiga.

Kara karanta wannan

An yaye tubabbun yan ta'addan Boko Haram 500 da aka yiwa horo

Ya ce amma yanzu da mutane suka fara komawa abin ya yi sauki.

Bugu da kari, jami'in yada labaran karamar hukumar Konduga, Asheikh Chabbol, ya ce Zakin ya fitittiki wasu manomi a kauyen Malari kuma su suka gayyaci mafarauta.

Yace:

"Mafarauta sun yi fito-na-fito da zakin kuma ya jiwa mutum biyu rauni kafin suka kasheshi. Suna jinya yanzu kuma an kai gawar zakin ma'aikatar yanayi."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel