Daliban zamani: Bidiyon matashi na yiwa tsohon hedimastansu izgili yayin da suka hadu

Daliban zamani: Bidiyon matashi na yiwa tsohon hedimastansu izgili yayin da suka hadu

  • Bidiyon wani dan Najeriya da ya yi wa tsohon shugaban makarantarsu zigili bayan da ya gamu dashi akan titi ya janyo cece-kuce a yanar gizo
  • Yayin da dalibin ke tuka motarsa daga gefe guda, matashin ya yiwa tsohon shugaban makarantar da ke kan acaba izgili
  • A cikin faifan bidiyon, tsohon shugaban makarantar ya yi kamar bai ji kiran da saurayin ke yi masa ba, sai ya kalli gefe kawai

Wani matashi dan Najeriya ya yi karo da tsohon shugaban makarantarsa na firamare inda ya yi amfani da damar da ya samu ta ci gaban rayuwa wajen yi masa izgili, lamarin da ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta.

Gajeren bidiyon da @gossipmilltv ya yada a Instagram ya fara ne daidai lokacin da wani dan Najeriya da ke tuka mota a bayan wani dan acaba da ke dauke da fasinja namiji yake magana.

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Ya Kamata Buhari Ya Miƙa Wa Mulki, In Ji Matasan Arewa

Dalibi ya kunya malaminsa a gaban duniya
Daliban zamani: Bidiyon dalibi na yiwa tsohon hedimastansu izgili yayin da suka hadu | Hoto: Alvarez, Instagram/@gossipmilltv
Asali: UGC

Daga nan ya taka motar tasa ya zo kusa da dan acaban kuma ya gane mutumin da ke baya a matsayin tsohon shugaban makarantarsu na firamare.

A bidion an ji matashin yana yi wa fasinja izgili, yana fada cikin harshen Yarbanci cewa tsohon shugaban makarantar shi ne malamin da a baya yace ba za su taba yin arziki ba ba tare da karatu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ci gaba da kiran fasinjan da ke kan babur din acaban da wani lakabi. Tsohon shugaban makarantar ya yi biris da kiran da saurayin ke masa gaba daya sannan ya juya fuskarsa zuwa gefe yana boye fuskarsa.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a kan wannan lamari

@___good___bhad___boi yace:

"Malam ya koya min littafi a makaranta... Malam bai ga aiki mai tsoka ba. Malam ya ganni a motata malam yayi kamar bai ganni ba. Malam nine dalibinka kar kaji kunya."

Kara karanta wannan

Ajiya maganin watarana: Dan Najeriya ya fasa asusunsa, kudin da ya tara sun girgiza intanet

@thonia_onopiri ya ce:

"Wannan ba abin ban dariya ba ne ko kadan, malamai, shugabannin makarantu, lakcarori da duk mutanen da suka ba mu ilimi ta kowace hanya a shekarun da suka wuce sun cancanci girmamawa daga gare mu komai wahalar da suka bamu, a wancan lokacin duk abin da suka yi sun yi ne don ganin mun zama mafi alheri ga al'umma."

@ralph_newrevelation ya ce:

"Matasan zamanin nan sun yi rashi. Wa ya horar da su, wa ya rene su...Aban kunya, ba da'a, ba iyaka. Gush!!"

@talk_anyhow_you_collect ya ce:

"Kaddarar kowa ta sha bamban akalla yana neman halal dinsa tunda ba satar kayan mutane yake ba."

Abin al'ajabi: Labarin Baturiyar da ta shekara 30 tana karantar da Hausa a Najeriya

A wani labrain, wata mata ‘yar kasar Holland da ta yi aikin wa’azin addinin kirista a Najeriya na tsawon shekaru 30, ta cika shekara 80 da haihuwa.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki ya bayar da gagarumin shawara ga ministocin Buhari

Abin da zai ba ku mamaki shine, matar mai suna Frances Boer ta yi aiki a yankin Arewacin Najeriya inda ta yi aiki a makarantun firamare tare da koyar da harshen Hausa.

An haifi Frances a kasar Holland a lokacin yakin duniya na biyu amma daga baya ta yi hijira zuwa Amurka sannan ta dawo Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel