Da ya bai wa mahaifinsa hantarsa, an yi aikin cike da nasara, sun yi hotuna cikin farinciki

Da ya bai wa mahaifinsa hantarsa, an yi aikin cike da nasara, sun yi hotuna cikin farinciki

  • Wani matashi ya bai wa mahaifinsa mai suna Deepak Hasija wani bangare na hantarsa domin ceton rayuwarsa
  • Mutumin mai suna Manya ya ce an yi aikin cike da nasara kuma mahaifinsa ya samu lafiya yayin da ya wallafa hotunansu tare
  • Labarin matashin ya taba zukatan jama'a a yanar gizo inda aka dinga kwarzanta shi ganin cewa ya nuna kauna da sadaukarwa ga mahaifinsa

Halayyar wani matashi na sadaukarwan da yayi ga mahaifinsa ya girgiza zukatan mutane da dama a kafafan sada zumuntar zamani.

Mutumin mai suna Manya Hasija ya kyautar da wani bangare na hantarsa ga mahaifinsa, Deepak Hasija wanda yayi matsananciyar jinya, sai dai anyi nasara a aikin.

Da ya bai wa mahaifinsa hantarsa, an yi aikin cike da nasara, sun yi hotuna cikin farinciki
Da ya bai wa mahaifinsa hantarsa, an yi aikin cike da nasara, sun yi hotuna cikin farinciki. Hoto daga LinkedIn/Humans of Bombay
Asali: UGC

Mutumin ya wallafa labarin nasa ne a LinkedIn, inda ya ce, an bai wa mahaifinsa rahoto mara dadin gani, wanda ke nuna yadda watanni kadan suka rage mishi a doron kasa.

Kara karanta wannan

Ajiya maganin watarana: Dan Najeriya ya fasa asusunsa, kudin da ya tara sun girgiza intanet

Labarin ya matukar karya zuciyar dan nasa, hakan yasa ya fara tunanin abunda ya kamata yayi. Inda ya yanke shawarar sadaukar da wani bangare na hantarsa ga mahaifinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce a LinkedIn: "Cikin sa'a, aka gwada aka ga yayi daidai, amma sai dai hantata tana da kitse da yawa. Dole sai na sadaukar da kashi 65 cikin dari na hantata kafin a samu ya rayu. Daga lokacin ba fara motsa jiki, gami da cin abinci mai kyau don in iya bashi. Bayan anyi min gwaje-gwaje da dama, aka shaida min cewa ina da da lafiyar da za a iya yin aikin!
"Hakan yasa ni cikin natsuwa matuka, sai dai bayan shaidawa mahaifina labarin mai dadi, fashewa yayi da kuka!"
"A yau, gashi dukkan mu muna da lafiya. Idan har labarin nan ya koyar damu wani abu, ba zai wuce rashin tabbacin rayuwa da kuma 'yan uwantaka ta jini da ta fi komai ba."

Kara karanta wannan

A kan bashin N2.7m da ta ke bin sa, magidanci ya nada wa matarsa mai juna biyu dukan mutuwa

Martanin jama'a kan wallafar

Masu amfani da kafafen sada zumuntar zamani sun yi tsokaci daban-daban bayan Humans of Bombay sun wallafa labarin, labarin ya samu dubbannin jinjina da tsokaci. Daga lokacin da aka rubuta wannan labarin, wallafar ta tattara jinjina kusan 60,000.

Ga wasu daga cikin tsokacin:

Ankit Kumar Gorain ya ce: "Na yarda da maganarka yallabai, babu wani abu da ke alakanta mutuntaka da tausayi."
Abhishek Paul yayi tsokaci: "Jiki na ya mutu gaba daya bayan jin wannan labarin!!!

Joseph Battaglia: "Abun burgewa ! Tsantsar soyayya! Babu abunda ya gagari Ubangiji, wanda wani zai iya wa wani, fiye da shimfida musu rayuwar su... Ok kasadar rasa rayuwa saboda su."

Asali: Legit.ng

Online view pixel