Da Dumi-Dumi: Hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen yan takarar gwamnan Ekiti na karshe

Da Dumi-Dumi: Hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen yan takarar gwamnan Ekiti na karshe

  • Hukumar zaɓe INEC ta fitar da jerin sunayen yan takarar jam'iyyu da zasu fafata a zaben gwamnan jihar Ekiti dake tafe
  • Hukumar ta kuma umarci duk jam'iyyar da ta ga babu sunanta ta gaggauta ankarar da ita a rubuce da sa hannun shugabanta na ƙasa
  • INEC ta shirya gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti ranar 18 ga watan Yuni, 2022

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen yan takarar gwamnan jihar Ekiti a zaɓen dake tafe ranar 18 ga watan Yuni, 2022.

INEC ta ce ta kafa sunayen yan takarar a ofisoshinta na jiha da kuma kananan hukumomi a Ekiti da kuma kafafen sada zumunta da doka ta amince da su.

Hukumar ta ce hakan ya yi dai-dai da abin da kundin dokokin zaɓe ya tanadar biyo bayan rufe karɓan ƴan takara daga jam'iyyun siyasa.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da yasa ban bayyana sha'awar gaje Buhari ba a hukumance, Bukola saraki

Hukumar INEC
Da Dumi-Dumi: Hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen yan takarar gwamnan Ekiti na karshe hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin watsa labarai, Festus Okoye, ya fitar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwan dai ta nuna INEC ta amince da Abiodun Abayomi Oyebanji a matsayin ɗan takarar jam'iyyar APC da mataimakinsa, Afuye Monisade.

Kazalika INEC ta tantance Olabisi Kolawole a matsayin ɗan takara na jam'iyyar PDP tare da Kolapo Olugbenga Kolade a matsayin mataimaki.

Wani sashin sanarwan ya ce:

"Tun a ranar Laraba, 16 ga watan Fabrairu, 2022, hukumar INEC ta fitar da sunayen ɗai-ɗaikun yan takara (Fom EC9) na zaben gwamnan jihar Ekiti a Ofisoshinta na jiha da kananan hukumomi."
"Bisa umarnin dokar zaɓe 2022, a yanzu hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen halastattun yan takara na ƙarshe biyo bayan karewar wa'adin karban yan takara daga jam'iyyu."
"INEC na tunatar da jam'iyyun siyasa cewa ƙarƙashin sashi na 32 (2), duk wacce ta ga babu sunan ɗan takararta ta sanar wa hukuma a rubuce da sa hannun shugabanta na ƙasa da Sakatare da Afidabit da bai wuce kwana 90 ba."

Kara karanta wannan

Borno: Sojoji Sun Gasa Wa Ƴan Ta'adda Aya A Hannu, Sun Kashe 10 Sun Ƙwato Bindigu Masu Harbo Jiragen Sama

Bugu da ƙari. INEC ta ja hankalin jam'iyyu kan sashi na 32 (3) na sabon kundin zabe 2022, wanda ya bayyana cewa rashin sanar da hukumar zaɓe, "Ba zai dakatar da zaɓe ba ko bata shi."

Jerin sunayen yan takara:

Sunayen yan takarar gwamnan Ekiti
Da Dumi-Dumi: Hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen yan takarar gwamnan Ekiti na karshe Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

A wani labarin na daban kuma Gwamnan Edo ya caccaki Wike kan kalamansa, yace PDP ba ta mutum ɗaya bace

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya ɗau zafi game da kalaman wuce gona da iri da gwamna Wike na Ribas ya yi a kan siyasar Edo.

Obaseki ya yi kira ga uwar jam'iyyar PDP ta ƙasa ta umarci Wike ya shiga taitayinsa ko kuma ya koya masa darasi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel