Fushin mahaliccina nake tsoro: Matashi ya mayar wa mai POS kudin da aka tura masa a kuskure

Fushin mahaliccina nake tsoro: Matashi ya mayar wa mai POS kudin da aka tura masa a kuskure

  • Wani dan Najeriya mai tsoron Allah ya mayar da N10,000 da mai POS ya tura masa da kuskure a Makurdi, jihar Benue
  • Mutumin mai suna Tavern Tersugh James ya ce ya yanke hukuncin mayar da kudin ne domin gujewa tsinuwar Allah
  • Taver ya ce wasu daga cikin abokansa sun shawarcesa da kada ya mayar da kudin saboda rabon shi ne ya tsaga, amma ya yi watsi da shawararsu

A yayin nuna gaskiya wacce ba koyaushe ake samu irin ta ba, wani dan Najeriya mai suna Taver Tersugh James ya mayar da N10,000 da mai POS ya tura masa bisa kuskure.

Wannan lamarin ya faru ne a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

Fushin mahaliccina nake tsoro: Matashi ya mayar wa mai POS kudin da aka tura masa a kuskure
Fushin mahaliccina nake tsoro: Matashi ya mayar wa mai POS kudin da aka tura masa a kuskure. Hoto daga Taver James
Asali: Facebook

Wani tsokaci da aka bayyanawa Legit.ng kai tsaye, ya nuna cewa an kusa cin zarafin mai POS din yayin da Taver ya yanke hukuncin mayar da kudin.

Kara karanta wannan

Obasanjo: Ban Nemi Mulki Ba, Mulki Ne Ta Riƙa Bi Na A Guje

Taver ya ce ya mayar da kudin ne gudun tsinuwar Ubangiji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abokai sun shawarce ni da kada in mayar

Taver ya ce wasu daga cikin abokansa sun shawarce sa kan kada ya mayar da kudin da aka sako masa bisa kuskure domin kawai Allah ne yayi da rabonsa. Ya ce sun shawarce sa kan kada ya mayar.

Sai dai kuma, ya yi watsi da shawararsu inda ya yanke hukuncin mayarwa

Kamar yadda sakon da aka tura wa Legit ya bayyana:

"Wani dan jihar Benue mara aikin yi kuma matashi mai suna Taver Tersugh James ya mayar da N10,000 da mai POS ya tura masa bisa kuskure a Makurdi, babban birnin jihar Benue.
"Ya bayyana cewa yana fatan Ubangiji ya amsa addu'ar wani ta wurinsa amma ba muguwar addu'a ba da za ta kawo masa tsinuwar Ubangiji ba. Ya kara da cewa, wasu daga cikin abokansa sun shawarcesa kan kada ya mayar da kudin inda suka jaddada cewa akwai hanyoyi masu yawa da Ubangiji ke sanya wa mutum albarkarsa. Amma ya bijirewa hakan kuma yace su bar irin wannan halin domin a samu al'umma ta gyaru.
"Duk da rayuwa ta yi tsanani, ya kara da cewa Ubangiji zai duba shi. Mai POS din wanda ubangidansa yace zai kwashe kudin daga albashinsa ya kwatanta matashin da mutumin arziki."

Asali: Legit.ng

Online view pixel