Yakin Rasha da Ukraniya zai tada Farashin kayan abinci a Najeriya, Asusun lamunin duniya IMF

Yakin Rasha da Ukraniya zai tada Farashin kayan abinci a Najeriya, Asusun lamunin duniya IMF

  • Yayinda yaki ke cigaba da gudana tsakanin Rasha da Ukraine, asusun lamunin duniya ta bayyana barazanar dake fuskantar Najeriya da sauran kasashen Afrika
  • A cewar IMF, Najeriya da sauran kasashen Afrika na gab da fara fuskantar hauhawar farashin kayan abinci da man fetur
  • Dirakta Manajar IMF ta bayyana cewa wannan yaki zai hana mutane zuwa nahiyar Afrika yawon ganin ido

Asusun lamunin duniya IMF ya bayyana cewa Najeriya da sauran kasashen Afrika na cikin halin barazanar tashin farashin kayan abinci, da man fetur sakamakon yakin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine.

Dirakta Manaja na IMF, Ms Kristalina Georgieva, ta bayyana hakan bayan ganawa da Ministocin kudin kasashen Afrika, gwamnonin bankuna kasa, wakilan majalisar dinkin duniya don tattauna illar da yakin Ukraine ka iya wa nahiyar, rahoton US News.

Kara karanta wannan

Yakin Rasha da Ukraine: Dangote ya shawarci FG kan matakin magance rashin abinci nan gaba kadan

Shugabar IMF
Yakin Rasha da Ukraniya zai tada Farashin kayan abinci a Najeriya, Asusun lamunin duniya IMF Hoto: REUTERS/Remo Casilli
Asali: Facebook

A jawabin da IMF,

"Yakin Ukraine na lalata rayukan miliyoyin mutane kuma yana gurgunta tattalin arzikin Ukraine. Yakin da takunkumin da aka kakabawa Rasha na da illa."
"Wannan na da illa ga Afrika. Mun tattauna yadda Afrika zata farfado. Afrika na fuskantar barazanar yakin Ukraine ta hanyoyi hudu - tashin farashin abinci, tashin farashin mai, rashin kudin shiga na yawn ganin ido, da kuma wuya samun harkalla da sauran kasashe."

A cewarta, asusun IMF shirya yake da taimakawa kasashen Afrika wajen dakile illolin yakin ta hanyar samar da tsare-tsare na shawari da bashi.

Yakin Rasha da Ukraine: Dangote ya shawarci FG kan matakin magance rashin abinci nan gaba kadan

Aliko Dangote, shugaban kanfanonin Dangote ya bukaci gwamnatin tarayya ta hana Najeriya siyar wa kasashen ketare masara don gudun karancin ta sanadiyyar yaki tsakanin Rasha da Ukraine.

Kara karanta wannan

Hajj da Umrah: Bukatar rigakafin Korona da wasu dokoki 6 ga Gwamnatin Saudiyya ta soke

Yayin martani ga tambayar da TheCable ta yi masa a taron karshen shekara na huda da kungiyar sarrafa abinci ta Najeriya ta shirya a ranar Alhamis, Dangote ya ce, Rasha da Ukraine sune manyan masu samar da sinadaran da ake amfani dasu wajen hada taki.

Ya ce, karancin wadannan sinadaran saboda yakin zai yi sanadin karancin taki da wasu kayayyakin abinci irin su; alkama da masara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel