Bayan watanni biyu, mutumin da aka yiwa dashen zuciyar Alade ya mutu

Bayan watanni biyu, mutumin da aka yiwa dashen zuciyar Alade ya mutu

  • Mutumin da ya kafa tarihi lokacin da aka yi masa dashin zuciyar alade watanni biyu baya ya mutu
  • David Bennett ya mutu ne lokacin da lafiyarsa ya sake tsanani bayan kwantar masa da hankalin cewa babu matsala
  • Iyalinsa sun bayyana cewa David Bennett ya sha bakar wahala amma bai yanke tsammani ba

Amurka - Watanni biyu bayan duniya ta yi murnar nasara a karon farko a tarihin harkar likitanci na yiwa dan Adam dashen zuciyar Alade, da alamun an samu koma baya.

Likitoci a asibitin jami'ar Maryland a ranar Laraba, 9 ga Febrairu, 2022, sun bayyana cewa David Bennet, mutumin da aka yiwa dashe, ya mutu bayan jikinsa ya tsananta.

Bayan watanni biyu, mutumin da aka yiwa dashen zuciyar Alade ya mutu
Bayan watanni biyu, mutumin da aka yiwa dashen zuciyar Alade ya mutu
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Ta Kacame: Mai Garkuwa Ya Yi Ƙorafi a Kotu, Ya Ce Abokansa Sun Cuce Shi Sun Bashi N200,000 Kacal Cikin N12m Da Suka Samu

Abinda Likitoci suka fadi

A jawabin da Asibitin ta saki, Likitocin sun bayyana cewa lokacin da suka gane David Bennet ba zai rayu ba,sai aka fara manejin jikinsa.

Har yanzu ba'a bayyana abinda yayi ajalinsa ba amma ana hasashen ba zai rasa alaka da dashen zuciyar da akayi masa ba.

'Dansa ya godewa Liktocin bisa kokarinsu.

A cewar 'dan, Likitocin sun yi namijin kokari wajen ganin mahaifinsa ya rayu.

Karon farko, an samu nasarar yiwa dan Adam dashin zuciyar Alade a Amurka

A baya mun kawo cewa karon farko a tarihi, Likitoci sun samu nasarar yiwa dan Adam dashin zuciyar Alade a jikin wani mutumin da aka fidda rai zai rayu.

Mutumin da aka yiwa dashin, David Bennet Sr, a birnin Maryland, kasar Amurka yana kwance yanzu yana murmurewa kawo ranan Litinin a asibitin jami'ar Maryland.

Diraktan dashin zuciya a asibitin, Dr Bartley Griffith, ya bayyanawa New York Times cewa:

Kara karanta wannan

Mai Mala bai bani wata wasika ba: Gwamna Neja ya yi martani mai zafi

"Tana bugawa, tana bada iskar da ake bukata, zuciyarsa ce kawai. Tana aiki sosai, mun ji dadi, amma bamu san abinda zai faru gobe ba. Ba'a taba irin wannan ba."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel