Yadda wasu mutum 18 suka yi nasarar tsallake mutuwa a jihar Kwara

Yadda wasu mutum 18 suka yi nasarar tsallake mutuwa a jihar Kwara

  • Allah ya kawo wani lamarin wuta da sauki yayin da wata Motar Bus dake tsakar tafiya a kan titi makare da mutane ta kama da wuta
  • Mutum 18 dake cikin motar sun samu nasarar tsira daga lamarin, amma kayan su baki ɗaya sun kone kurmus a ciki
  • Kwamandan hukumar kare haɗurra na jihar Kwara ya ce dole ta sa suka tsayar da motoci a kan hanyar domin shawo kan wutar

Kwara - Wasu mutane 18 sun ga tashin hankali kuma lamarin ya zo da sauƙi yayin da Motar Bus mai ɗaukar mutum 18 da suke ciki ta kama da wuta ta cikin zabga gudu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, lamarin wanda ya auku a ƙauyen Koko Araromi, kan hanyar Ajase Ipo, jihar Kwara ya bar matafiya da direbobi a tsaye.

Kara karanta wannan

Wajibi APC ta fita tsara a cikin jam'iyyu, Bola Tinubu ya yi magana kan rikicin shugabancin APC

Hadarin Bus
Yadda wasu mutum 18 suka yi nasarar tsallake mutuwa a jihar Kwara Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Motar Bas ɗin, wacce rahoto ya nuna cewa tana kan hanyar zuwa garin Osdogbo a jihar Osun ta kama da wuta ne da misalin ƙarfe 10:57 na safe ana cikin zabga tafiya.

Allah ya kawo abun da sauki, domin duk da ba'a rasa rayuka ba kasancewar Mutanen cikin motar sun yi gaggawar fita, amma duk kan kayan su da suke tafe da su a motar sun kone kurmus.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane matakin hukumomi suka ɗauka?

Shugaban rundunar hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kwara, Jonathan Owoade, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a wata hira ta wayar salula.

Owoade wanda ya alaƙanta kama wutar motar da yoyon man Fetur ɗin motar, ya bayyana cewa:

"Jami'an hukumar kare haɗurra FRSC sun ɗauki matakin dakatar da motoci masu tafiya a kan hanyar na tsawon mintuna saboda wutar dake ci a Bas ɗin, hakan ya zame musu wajibi."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mutane sun rasa rayukansu yayin da Tankar Fetur ta fashe kusa cibiyar mu'ujiza MFM

A wani labarin na daban kuma Dandazon matafiya sun kwanta dama yayin da Tankar Fetur ta fashe kusa da MFM

Wani mummunan hatsari fiye da ɗaya da ya auku a wuri ɗaya ya lakume rayukan matafiyan dake kan hanyar da dama.

Haɗarin wanda ya rutsa da motocin hawa biyu da kuma Tankar dakon man Fetur ya faru ne a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel