Legas: Matashiyar Da Ake Zargi Da Kisar Kai Ta Lashe Gasar Sarauniyar Kyau a Gidan Yarin Kirikiri

Legas: Matashiyar Da Ake Zargi Da Kisar Kai Ta Lashe Gasar Sarauniyar Kyau a Gidan Yarin Kirikiri

  • Wata matashiyar budurwa, Chidinma Ojukwu wacce a watannin baya aka zarge ta da kisan mai gidan talabijin din Super TV, Michael Ataga ta zama sarauniyar kyau ta gidan yarin Kirikiri
  • Ojukwu ta shiga gasar sarauniyar kyau tare da sauran matan da ke zaune a gidan yarin inda ta lashe gasar kamar yadda Kakakin hukumar gidan yari na kasa, Francis Enobore ya tabbatar
  • Kakakin ya ce an shirya gasar ne don tabbatar da walwalar mazauna gidan yarin kuma an fara shirya gasar kyau, girke-girke, wasanni da sauran su ga mazauna gidan yari

Legas - Wata budurwa, Chidinma Ojukwu, wacce aka dinga yada labarinta a watannin baya ana zargin ta da kisan Super TV, Michael Ataga, ta lashe gasar sarauniyar kyau na gidan gyaran halin Kirikiri ta shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a Kaduna, rayuka sun salwanta

Ojukwu ta shiga cikin gasar tare da sauran matan da ke zaune a gidan gyaran halin wanda ta lashe gasar, kamar yadda The Punch ta rahoto.

Legas: Matashiyar Da Ake Zargi Da Kisar Kai Ta Lashe Gasar Sarauniyar Kyau a Gidan Yarin Kirikiri
Legas: Budurwar Da Ake Zargi Da Kisar Kai Ta Lashe Gasar Sarauniyar Kyau a Gidan Yarin Kirikiri. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

A wata tattaunawa da Daily Trust ta yi da kakakin gidan gyaran hali na kasa, Francis Enobore, ya tabbatar da labarin har ya bayyana dalilin yin gasar.

Enobore ya tabbatar da labarin gasar kyawun

Kakakin ya kula da yadda aka shirya gasar don tabbatar da walwalar mazauna gidan yarin. Enobore ya kara da cewa ana shirya gasar kyau, girke-girke da sauran su don a sa ‘yan gidan yarin nishadi.

Kamar yadda ya ce:

“Gasar wata hanya ce ta kawo gyara a gidajen gyaran hali don sanya mazauna cikin sa cikin halin nishadi. Kuma muna shirya gasa irin hakan don wasun su zasu iya samun damar ayyuka a fagen nishadi.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan sanda sun mutu yayin da motar tawagar ministocin Buhari ta yi hadari

“Akwai shirye-shirye da muka fara hadawa don faranta wa mazauna gidan yari rai da kuma kwantar musu da hankali. Bama so kadaici ya halaka su don haka muke kawo shirye-shiryen da zasu debe musu kewa.
“Muna koyar da su dinki, kwalliya da sauran su. Hakan yana matukar faranta musu musamman wadanda suke lashe gasar.
“Kuma musamman mazauna gidan gyaran halin Kirikiri suna matukar shiga gasar kuma suna samun nasarori iri-iri.”

Ni Ce Wacce Tafi Kowa Taurin Kai a Najeriya, Jaruma Bayan Ta Ci Gaba Da Wallafe-Wallafe Kan Regina Daniels

Alamu suna nuna cewa rikicin jarumar Nollywood, Regina Daniels da fitacciyar mai sayar da maganin mata, Hauwa Saidu wacce aka fi sani da Jaruma, bai kusa zuwa karshe ba.

Mutane da dama sun yi tunanin Jaruma za ta fita daga harkar Regina tun bayan sakin ta daga gidan yari da aka yi a makon da ya gabata, amma ba hakan bane.

Kara karanta wannan

Obasanjo: Galibin Masu Son Zama Shugaban Ƙasa Ya Kamata Suna Ɗaure a Gidan Yari

A wannan karon, Jaruma ta wallafa hoton ta da na Jarumar Nollywood din yayin da take tallata mata kayan sana’arta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel