Ni Ce Wacce Tafi Kowa Taurin Kai a Najeriya, Jaruma Bayan Ta Ci Gaba Da Wallafe-Wallafe Kan Regina Daniels

Ni Ce Wacce Tafi Kowa Taurin Kai a Najeriya, Jaruma Bayan Ta Ci Gaba Da Wallafe-Wallafe Kan Regina Daniels

  • Fitacciyar mai sayar da maganin mata, Hauwa Saidu Mohammed wacce aka fi sani da Jaruma ta ci gaba da wallafa hotunan Regina Daniels
  • Da alama Jaruma, wacce bata dade da fitowa daga gidan gyaran hali ba, bata shirya daina wallafe-wallafen da suka janyo mata matsala a kwanakin baya ba
  • Mai maganin matan ta kira kanta da mutum mafi taurin kai a gaba daya Najeriya, ta ce bata damu da matsalolin da zasu biyo baya ba

Alamu suna nuna cewa rikicin jarumar Nollywood, Regina Daniels da fitacciyar mai sayar da maganin mata, Hausa Saidu wacce aka fi sani da Jaruma, bai kusa zuwa karshe ba.

Mutane da dama sun yi tunanin Jaruma zata fita daga harkar Regina tun bayan sakin ta daga gidan yari da aka yi a makon da ya gabata, amma ba hakan bane.

Kara karanta wannan

Bidiyon jaruma Umma Shehu tare da diyarta yayin da suke girgijewa ya haifar da cece-kuce

Ni Ce Wacce Tafi Kowa Taurin Kai a Najeriya, Jaruma Bayan Ta Ci Gaba Da Wallafe-Wallafe Kan Regina Daniels
Ni Ce Wacce Tafi Kowa Taurin Kai a Najeriya, Jaruma Bayan Ta Ci Gaba Da Wallafa Kan Regina Daniels. Hoto: @jaruma_empire
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wannan karon, Jaruma ta wallafa hoton ta da na Jarumar Nollywood din yayin da take tallata mata kayan sana’arta.

Jaruma ta ci gaba da shimfida karkashin hoton inda tace ta fi kowa taurin kai a Najeriya.

Ta bayyana yadda ta biya Regina Naira miliyan 10 don ta tallata mata hajar ta inda tace akwai wasu wallafe-wallafe 87 na tallace-tallacen da Regina ta mata wadanda za ta saki.

Ga abin da ta wallafa:

‘Yan Najeriya sun yi tsokaci baya Jaruma ta ci gaba da wallafa akan Regina Daniels

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin tsokacin jama’a wadanda suka bayyana mamakin su akan wannan halin na Jaruma.

chychy_ibe ya ce:

“Abin nan bai bani dariya ba. Da alamu matsala take so ta sa kan ta, idan yanzu aka kara kama ta sai wasun ku su fara tausaya mata a dinga cewa an yi amfani da karfi akan ta amma yanzu ta ki ta kama kan ta.”

Kara karanta wannan

Wani hanin: Bayan shekaru 12 tana dako, Allah ya azurta mata da haihuwar 'ya'ya hudu nan take

gloria.bpalmeragoye tace:

“Ko wanene yake amfani da shafin nan ya kula. Batun kukan ta a gidan yarin Suleja bai kare ba. Ya kamata ta kama kanta ta kuma fuskanci gaskiya.”

fantelle_mercy tace:

“Ina mamakin kasuwancin da Jaruma take yi. Ta daina surutai ta mayar da hankalin ta akan sana’ar ta.”

sleekvalerie ta yi tsokaci, inda tace:

“Ta dinga kera wa mabiyan ta karya. Ta daina asarar kudaden ta a banza.”

Jaruma Ta Magantu Bayan Alƙali Ya Umarci a Sake Kama Ta

Tunda farko, Hauwa Muhammad, sananniyar mai maganin-mata wacce aka fi sani da Jaruma ta bayyana dalilinta na rashin zuwa babbar kotun Zuba da ke Abuja don ci gaba da shari’a, The Cable ta ruwaito.

Tun a watan da ya gabata, ‘yan sanda sun kama Jaruma da laifin cin mutunci, yada karairayi da kuma bata sunan biloniya Ned Nwoko.

Amma bayan gurfanar da ita, kotu ta bayar da belin ta bayan ta kwashe kwana hudu a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Wata mata a Nasarawa: Dalilin da yasa na amince da na ya dirka min ciki

A ranar Laraba ya kamata a ci gaba da sauraron karar, sai dai Jaruma bata bayyana a gaban kotu ba hakan yasa alkali Ismailia Abdullahi ya bukaci a kara kamo ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel