Ana hango tsada da wahalar abinci a Najeriya yayin da damina ta ke shirin shigowa

Ana hango tsada da wahalar abinci a Najeriya yayin da damina ta ke shirin shigowa

  • Manoma su na kokawa a game da yadda buhun takin zamani ya yi matukar tsada a kasuwa a yau
  • Idan har farashin taki bai yi kasa ba, akwai yiwuwar mutane su saye kayan abinci da tsada a kasar
  • Yakin Rasha da Ukraine yana cikin abubuwan da zai taimaka wajen kawo matsalar abinci a 2022

Nigeria - Masu ta-cewa a harkar noma, musamman manoma su na tsoron cewa za a iya fuskantar wahalar abinci idan abubuwa suka cigaba da tafiya a haka.

Wani dogon rahoto da Daily Trust ta fitar ya nuna ana fama da tsadar farashin takin zamani. Idan har ba a dauki mataki ba, hakan zai yi tasiri a noman bana.

Manoma su na jin tsoron idan buhun takin zamani ya cigaba da yin tsada, mutane da yawa ba za su girbe kayan gonan da ake bukata a kakar shekarar nan ba.

Kara karanta wannan

Babu maganar janye yajin-aiki, kungiyar ASUU ta gindayawa Gwamnatin Najeriya sharadi

Shugaban kungiyar manoma na kasa na AFAN, Arc. Kabiru Ibrahim ya ce a shekarar da ta gabata, manoma ba su samu rahusa wajen sayen takin zamani ba.

Kabiru Ibrahim ya shaidawa manema labaran cewa muddin aka cigaba da sayen taki da tsada, to ya zama dole kayan amfanin gona su kara kudi idan sun fito.

Gona shar
Wata gona a kasar waje Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Taki ya yi tsada a yau

Shugaban kungiyar TOGAN ta manoma tumaturi a Najeriya, Alhaji Sani Danladi Yadakwari ya ce manoma su na fatan taki zai sauko kafin shigowar damina.

A jihohi da-dama, ana saida buhun Urea ne tsakanin N11, 000 zuwa N18, 000. Haka zalika farashin duk buhun NPK yana yawo tsakanin N10, 000 da N16, 000.

A daminar bara, an saida buhun NPK ne kusan N9000 yayin da aka saida na Urea a kan N10000.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: An Sanar Da Ranar Da Rasha Da Ukraine Za Su Yi Zaman Tattauna Tsagaita Wuta

Yakin Rasha v Ukraine

Kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto, yakin Rasha da Ukraine zai iya tasiri wajen farashin kaya a Najeriya. Daga ciki har da kudin takin zamani.

Najeriya ta na shigo da kashi 37% zuwa 45% na kayan da ake hada takin Urea ne daga kasar Ukraine, kusan 35% kuma na kayan su na zuwa ne daga Moroko.

Ina tsarin PFI?

Abubakar Sani Abdullahi, wani malamin gona a jami’ar ABU Zaria ya bayyana cewa tun bayan rasuwar Abba Kyari ake fama da tsadar buhun taki a kasar nan.

A karkashin tsarin Presidential Fertiliser Initiative da gwamnatin nan ta kawo, manoma su na samun taki da araha. A halin yanzu abubuwa sun tsaya a Najeria.

Rashin tsaro

An ji cewa jami'an tsaro su na yi wa Sojojin Boko Haram raga-raga a Arewa maso gabashin Najeriya, yanzu ‘yan ta’adda sun fara addabar irinsu kasar Kamaru.

Kara karanta wannan

Muna Da Huja Da Ke Nuna PDP Ce Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2019, in Ji Ayu

A shekarar bara, Boko Haram ta kai hari sau 37 a Kamaru, ta kashe mutane kusan 60. A nan, matsalar rashin tsaro ta fi kamari yanzu a yankin Arewa ta yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel