Hotuna da bidiyon ranar bakin ciki ga Abba Kyari yayin da ya bayyana a gaban kotu

Hotuna da bidiyon ranar bakin ciki ga Abba Kyari yayin da ya bayyana a gaban kotu

  • Dakataccen babban dan sandan da ya sha yabo saboda kwazonsa a baya, Abba Kyari, ya bayyana gaban babbar kotun tarayya a Abuja
  • An ga fitaccen dan sandan sanye da manyan kaya kuma ya bayyana a gaban kotu da takunkumin fuska yayin da ake tuhumarsu da zargin safarar miyagun kwayoyi
  • A bidiyon da ya bayyana, an ga dan sanda yana ta sunkuyar da kai a kokarinsa na kare fuskarsa daga na'urar nadar sauti da hotuna a kotun

FCT, Abuja - Dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sandan Najeriya kuma shugaban rundunar binciken sirri, DCP Abba Kyari, ya gurfana a gaban babban kotun tarayya dake Abuja a ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Kyari ya bayyana a gaban kotun tare da wasu 'yan sandan rundunar IRT da aka kama da zargin safarar hodar Iblis.

Kara karanta wannan

Don Allah kada ku kai mu magarkama: Abba Kyari da 'yan tawagarsa sun roki kotu

A karar mai lamba FHC/ABJ/57/2022, an zarge su da hada kai wurin aikata laifi, kangewa da kuma harkar safarar hodar Iblis da ta kai nauyin 17.55Kg.

Ga hotunansu a gaban kotun.

Hotunan ranar bakin ciki ga Abba Kyari yayin da ya bayyana a gaban kotu
Hotunan ranar bakin ciki ga Abba Kyari yayin da ya bayyana a gaban kotu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Hotuna da bidiyon ranar bakin ciki ga Abba Kyari yayin da ya bayyana a gaban kotu
Hotuna da bidiyon ranar bakin ciki ga Abba Kyari yayin da ya bayyana a gaban kotu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A bidiyon da jaridar The Nation kuwa ta wallafa a shafinta na Twitter, an ga dakataccen babban dan sandan yana sunkuyar da kai yayin da ake kokarin nadar bidiyon.

Ya bayyana a kotun ne sanye da kaftani mai kalar duhu kuma ya sakaya fuskarsa da takunkumin fuska.

Ga bidiyon ku kashe kwarkwatar idon ku:

DCP Abba Kyari da mutum 6 sun bayyana a kotu, za a gurfanar da su

A wani labari na daban, Abba Kyari da wasu mutane shida da ake zargi da hannu wajen badakalar miyagun kwayoyi sun bayyana a harabar babban kotun tarayya a Abuja.

Kara karanta wannan

Kano: Mummunar gobara ta lamushe kadarorin N18m a Mariri

The Nation ta kawo rahoto a safiyar Litinin, 7 ga watan Maris 2022 cewa DCP Abba Kyari sun shigo kotu, ana sauraron a gurfanar da su a gaban Alkali. Jami’an hukumar NDLEA mai yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ne suka kai Kyari da ragowar ‘yan sanda da mutane biyu da ake zargi zuwa kotu.

Dakarun NDLEA biyu da suka jagoranci wadannan mutane da ake tuhuma, su na dauke da makamai.

Jaridar ta ce an ga Abba Kyari sanye da tufafi mai launin tsanwa a harabar kotun. Jami’in ‘dan sandan ya hallara ne a cikin wata katuwar motar gwamnati.

Ragowar mutane hudun da za ayi shari’a da su a zaman yau sun iso ne a cikin wasu motocin Hilux. A halin yanzu duk su na jiran zuwan malaman shari’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel