Da dumi-dumi: Nine mukaddashin Shugaban APC, cewar Gwamnan Neja bayan jita-jitar tsige Mai Mala Buni

Da dumi-dumi: Nine mukaddashin Shugaban APC, cewar Gwamnan Neja bayan jita-jitar tsige Mai Mala Buni

  • Ta faru ta kara, gwamnan Neja ya bayyana cewa shine mukaddashin shugaban jam'iyyar APC
  • Wannan sabuwar dambarwa na aukuwa ne ana saura makonni biyu taron gangamin jam'iyyar mai ci
  • Daga shiga ofis, Gwamnan Neja ya rantsar da shugabannin jam'iyya na jihohin Najeriya 36 da Abuja

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya zama Shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) bayan tunbuke Gwamna Mai Mala buni na Yobe.

Mai Mala Buni, wanda rahotanni suka nuna cewa yana kasar Dubai yanzu, ya rike kujerar na tsawon shekaru biyu.

Gwamna Bello daga danewa kujerar matsayin mukaddashin ya rantsar da sabin shugabannin jam'iyyar APC na jihohi a zamansa da sauran mambobin kwamitin rikon kwaryan.

Wannan ya bayyana a bidiyon Sakataren yada labaran gwamnan Mary Noel-Berje.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta yi amai ta lashe, tace har yanzu Gwamna Mala Buni ne shugabanta

Da dumi-dumi: An tsige Mai Mala Buni daga kujeran Shugaban APC
Da dumi-dumi: An tsige Mai Mala Buni daga kujeran Shugaban APC
Asali: Facebook

Daga cikin wadanda ke hallare a zaman akwai Shugaban matasan jam'iyyar APC kuma hadimin shugaba Buhari, Barista Isma'il Ahmad, Farfesa Tahir, Sanata Yusuf Yusuf na Taraba, dss.

Gwamna Bello a jawabinsa ya yi kira da sabbin shugabannin APC na jihohi su hada kan mambobinsu na jiha kuma su daina rikici tsakaninsu.

Yace:

"Ina taya ku murna kuma Shugaba Muhammadu Buhari na tayaku murna. Ina kyautata zaton cewa idan kuka koma jihohinku, zaku hada kan 'yayan jam'iyya."
"Dan Allah a manta da rikice-rikicen baya, wajibi ne ku hada kan kowa don samun sakamako mai kyau a zaben 2023."

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel