Kisan Hanifa: Shaidu sun gabatar da abubuwa 10 da suka gano game da makasan Hanifa a Kotu

Kisan Hanifa: Shaidu sun gabatar da abubuwa 10 da suka gano game da makasan Hanifa a Kotu

  • A zaman cigaba da sauraron ƙara kan kisan Hanifa Abubakar, gwamnatin Kano ta fara gabatar da shaidu
  • A ranar Laraba, Shaidu uku da aka gabatar sun mika wa Kotu abubuwa 10 da suka kwato a hannun waɗan da ake zargi
  • Bayan sauraron kowane bangare da kuma shaidun, Alkalin Kotun ya dage zaman zuwa Ranar Alhamis, 3 ga watan Maris

Kano - A jiya Laraba aka sake gurfanar da mutanen da ake zargi da kashe Hanifa Abuɓakar a Kotun Kano domin fara sauraron shaidu.

Jaridar The Guardian ta rahoto cewa Shaidun sun gabatarwa Kotu abu 10 da suka gano game da lamarin kisan yarinyar yar shekara 5.

Ana tuhumar mutanen da ake zargi, Abdulmalik Tanko, Hashimu Isiyaku, da Fatima Musa da laifin garkuwa, kisan kai, haɗa baki, da sauran su.

Kara karanta wannan

Kisan gillar Hanifa: An hana 'yan jarida daukar rahoton zaman kotu

Tanko da Hanifa
Kisan Hanifa: Shaidu sun gabatar da abubuwa 10 da suka gano game da makasan Hanifa a Kotu Hoto: gistreel.com
Asali: UGC

Duk da Tanko da Isyaku sun musanta zargin kashe Hanifa da sauran tuhuma in banda haɗa kai wurin aikata laifi, ita Fatima Musa ta musanta baki ɗaya tuhumomi 5 da ake mata.

Yayin cigaba da zaman, Antoni Janar kuma Ministan Shari'a na jahar Kano, Lawal Abdullahi, ya gabatar da shaidu uku gaban Mai Shari'a, Usman Na'abba a babbar kotun Kano 5.

Shaidu ukun sune, jami'an hukumar DSS guda biyu da kuma Insufektan yan sanda, kuma sun ba da shaida tare da miƙa wa Kotu abubuwa 10 da za su tabbatar da abin da suka faɗa kan waɗan da ake zargi.

Waɗan ne abubuwa ne shaidun suka gabatar?

Abubuwan da shaidun suka gabatar wa Kotun sun haɗa da, wayoyin hannu guda huɗu, Cebur, kayan makarantar Hanifa, Kananan Hotuna, da kuɗi N30,300 da suka gano tare da Tanko.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Shugaba Buhari ya amince da dala miliyan $8.5m na kwaso yan Najeriya daga Ukraine

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman Kotu da ya shafe awa 6, lauyan dake kare waɗan da ake ƙara, Muktar Umar, ya ce za su cigaba da bin shari'ar har karshe.

Ya ce sun yi wa shaidun tambayoyi domin tabbatar da gaskiyar abin da suka yi ikirari a gaban Kotu.

A bangarensa, Lauyan gwamnati, wanda ya kwashe wa'adi biyu a matsayin Antoni Janar na Kano, ya ce za su ƙara gabatar da shedu a zama na gaba.

"Akwai karin shaidu uku da zamu gabatar a zaman Kotu na gaba."

Daga nan sai Alkali Na'abba ya ɗage zaman har zuwa ranar 3 ga watan Maris, 2022, yau kenan, domin cigaba.

A wani labarin na daban kuma Dakarun Rasha sun zagaye birnin da Daliban Najeriya ke ciki a Ukraine

Akalla daliban Najeriya 370 dake karatu a ƙasar Ukraine suka makale a birnin Sumy yayin da Dakarun Rasha suka zagaye birnin.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Bam Ya Sake Fashewa a 'Kauyen Jihar Niger

Sakataren Ofishin jakadancin Ukraniya a Najeriya yace ya kamata FG ta tashi tsaye matukar tana son ceton ɗaliban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel