Duka Gwamnonin APC za su yi zaman musamman domin dinke sabuwar baraka kan mukamai

Duka Gwamnonin APC za su yi zaman musamman domin dinke sabuwar baraka kan mukamai

  • A ranar Talatar nan ake sa ran duka Gwamnonin APC za su hallara a garin Abuja domin wani taro
  • Gwamnonin za su daddale magana a kan yadda aka yi rabon mukamai na kasa a majalisar NWC
  • Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC su na ganin akwai gyara game da kason da aka ji jam’iyyar tayi

Abuja – Dazu nan mu ke jin cewa Gwamnonin jam’iyyar APC 21 za su yi taro a babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata, 1 ga watan Maris 2022.

Jaridar The Cable ta ce gwamnonin jihohin jam’iyyar APC mai mulki za su hadu ne domin su tattauna kason kujerun da aka yi a zaben shugabanni.

Wasu daga cikin gwamnonin APC sun koka a kan yadda aka ware kujerun da za a ba kowane bangare, su na ganin ba a bi umarnin shugaban kasa ba.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Ni da wasu gwamnoni 5 za mu sayo na’urorin harba makamai daga Turkiyya don murkushe 'yan binidiga

Wani gwamna da ke mulki a Arewacin Najeriya ya shaidawa The Cable cewa kason da aka yi bai nuna an yi musayar kujeru tsakanin yankunan kasar ba.

“Idan kun lura babu wanda ya sa hannu a wannan jerin da yake yawo a kafafen sada zumunta. Babu wanda aka alakanta da takardar.”
“Gwamna Nasir El-Rufai ya ce Arewa da Kudu za su yi musayar mukaman da suka rike, amma jerin da aka fitar bai nuna an yi musaya ba.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- inji Gwamnan

Gwamnonin APC
Wasu Gwamnonin APC Hoto: @Hon Surajo Tijjani Cycle
Asali: Facebook

A cewar gwamnan, idan da an yi aiki da wannan tsari, Sakataren jam’iyya zai fito ne daga kudu maso gabashin Najeriya, ba Kudu maso yamma da ake fada ba.

An saba dokar jam'iyya

Wani Sanata ya koka a kan zaben shiyyoyi da aka shirya za ayi a ranar 12 ga watan Maris. Sanatan ya ce a dokar da APC take amfani da shi, babu shiyyoyi.

Kara karanta wannan

Okorocha ya bada shawarar yadda za a magance rikicin APC ko APC tayi asarar Biliyoyi

Sanatan ya ce ba za a fara aiki da shugabannin shiyyoyi ba sai bayan an yi zaben shugabanni na kasa tukuna. Dole sai an jira an sa wa sabon tsarin mulki hannu.

Wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar, ya ce abubuwan da za a tattauna a wajen wannan taro na goben sun hada har da lokacin zabe da hukumar INEC ta fitar.

2023 sai Tinubu

Dazu aka ji shugabar kungiyar Arewa Women for Bola Tinubu ta ce Jigon APC ne Magajin Muhammadu Buhari domin ba wai maganar shekaru ake yi ba.

Saadatu Dogonbauchi ta fitar da wani jawabi, tana bayanin abin da ya sa Bola Tinubu ya fi kowane ‘dan takarar shugaban kasa cancanta a zaben shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel