Rikicin fili: ABU Zaria ta na barazanar kai Gwamna gaban Alkali a dalilin saba umarnin kotu

Rikicin fili: ABU Zaria ta na barazanar kai Gwamna gaban Alkali a dalilin saba umarnin kotu

  • Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria ta na shirin sake shigar da karar Gwamnatin Nasir El-Rufai a kotu
  • Hakan na zuwa ne bayan KASUPDA sun yi watsi da umarnin kotu, sun fara ruguza filin DAC a Mando
  • Ana rigima tsakanin ABU Zaria da Nasir El-Rufai a kan mallakar filin da aka gina kwalejin jami'ar

Kaduna - Shugabannin jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke garin Zaria su na barazanar kai karar gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai zuwa kotu.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 16 ga watan Fubrairu 2022, inda aka ji jami’ar ta na zargin Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da raina kotu.

A watan Junairun 2022 Alkali mai shari’a, K. Dabo na babban kotun jihar Kaduna da ke garin Zaria ya bada umarni cewa gwamnati ta dakata daga taba filin.

Kara karanta wannan

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

Alkalin ya haramtawa gwamnan Kaduna da kwamishinan shari’a da sauran ma’aikata da dillalai haurawa cikin filin wannan makaranta, amma ba a bi umarnin ba.

Rahoton ya ce a ranar Talata an ga jami’an KASUPDA a cikin filin, su na rushe katangar da ABU ta gina.

Rikici: ABU Zaria ta na barazanar kai wani Gwamna gaban Alkali kan saba umarnin kotu
Farfesa Kabiru Bala da Nasir El-Rufai Hoto: ABU Zaria, kasu.edu.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za mu hadu a kotu - ABU

ABU Zaria ta aikawa hukumomin KASUPDA da KADGIS takarda ta hannun lauyoyinta, Maakees Chambers, ta na sanar da su cewa za ta sake kai karar su a kotu.

Da aka tuntubi shugaban hukumar KADGIS na jihar Kaduna, Altine Jibrin, ta ce ba za ta ce komai a kan maganar ba saboda a halin yanzu ana kan shari’a a kotu.

Haka zalika ‘yan jarida sun nemi jin ta bakin mai magana da yawun KASUPDA, Nuhu Garba wanda ya bayyana cewa zai fitar da jawabi a lokacin da ya dace.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya cika shekaru 62 a duniya, gwamnonin APC sun aike masa da sako

Tarihin rigimar filin

Tun tuni ake ta rigima tsakanin wannan jami’a da gwamnatin El-Rufai a kan wani fili mai tsawon shekta 196, 258 wanda jami’ar ta ke ikirarin cewa na ta ne.

A wannan fili da ke Mando, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna ne jami’ar ABU ta gina kwalejin noma da kiwon dabbobi tun shekara da shekaru da suka wuce.

Hukumar KADGIS ta na ikirarin cewa an yanka wannan fili ne zuwa fuloti sama da 520 domin al’umma su gina gidajen zama, shaguna da wuraren shakatawa

Shari'ar Gwamnoni da Buhari

Ku na da labarin cewa Kayode Fayemi ya fadi dalilinsu na shiga kotun Allah ya isa da Gwamnatin tarayya domin raba masu gardama a kan dokar E.O 10.

Shugaban NGF ya zargi wasu Mukarrabai da ba Muhammadu Buhari gurguwar shawarar da ta sabawa dokar kasa, don haka aka raba masu gardamar ta su a kotu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Naɗa Mohammed Bello Koko a Matsayin Shugaban NPA Mai Cikakken Iko

Asali: Legit.ng

Online view pixel