Mikawa Amurka Abba Kyari: Daga karshe, Antoni Janar Abubakar Malami ya yi magana

Mikawa Amurka Abba Kyari: Daga karshe, Antoni Janar Abubakar Malami ya yi magana

  • Abubakar Malami ya tabbatar da labarin yanke shawarar mikawa Amurka jami'an dan sandan da aka dakatar Abba Kyari
  • Malami yace takardar mika Abba Kyari ta isa ofishinsa kuma suna abubuwan da ya kamata a kai
  • Antoni Janar na tarayya yace ya gamsu da cewa babu siyasa cikin bukatar da Amurka ke yiwa Abba Kyari

Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malam, ya yi magana kan shirin mikawa gwamnatin Amurka dakataccen dan sanda, DCP Abba Kyari.

Malamin, wanda yayi magana da bakin mai magana da yawun Malami, Isa Gwandu, ya bayyana cewa bayan dubi mai zurfi cikin lamarin, an mika bukatar zuwa hukumomi don daukan mataki.

Antoni Janar Abubakar Malami
Mikawa Amurka Abba Kyari: Daga karshe, Antoni Janar Abubakar Malami ya yi magana Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta amince a mikawa Amurka Abba Kyari

Daily Trust ta ruwaitosa da cewa:

"Game da bukatar (mikashi) da abubuwan dake kunshe ciki, an tattara takardun kuma an mikawa hukumomin da suka dace don daukar matakin da ya kamata."
Kamar yadda kuka sani mika mutum hannun wata kasa na da matakai daban-daban."
Ofishin Antoni Janar na kasa kuma Ministan Shari'a ta karbi takardar bukatar mika jami'in da ake magana (Abba Kyari)

Gwamnatin tarayya ta amince a mikawa Amurka Abba Kyari

Kun ji cewa gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta amince da bukatar Amurka, na a mika mata dakataccen DCP na yan sanda, Abba Kyari, bisa alakarsa da shahrarren dan damfara Abass Ramon aka Hushpuppi da wasu mutum hudu.

Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN) ya bayyana hakan a karar da ya shigar gaban shugaban Alkalan babban kotun tarayya dake Abuja kan lamarin, rahoton Vanguard.

An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/249/2022 karkashin dokar Extradition Act.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya dira birnin Nairobi, inda daga nan zai tafi Landan ganin Likita

Wannan kara da ya shigar ya biyo bayan bukatar Abba Kyari da wakilin jakadan Amurka yayi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel