Yajin aikin Likitoci: Sabon jariri ya mutu a asibiti sakamakon rashin Likita
- Wannan jariri ya mutu a jihar Legas bayan an nemi Likitoci an rasa a asibitoci
- Likitoci a fadin Najeriya sun tafi yajin aiki ranar Alhamis
- A daidai wannan lokaci shugaban kasa ya garzaya Landan don duba lafiyarsa
Mutuwar wani sabon jariri a asibitin koyarwan jami'ar Legas (LUTH) sakamakon yajin aikin da Likitocin Najeriya ke yi ya janyo cece-kuce a fadin kasar.
Wani mutumi mai suna Vincent Abuladan ya bayyana yadda surukarsa ta samu mishkila yayin nakuda kuma aka rika yawo da ita daga asibiti zuwa asibiti amma babu Likitoci har inda yaron ya mutu a asibitin LUTH.
A cewar TheCable, Vincent ya daura laifin mutuwar sabon jaririn kan rashin Likitoci a asibitocin da suka je.
Ya ce ko a asibitin karshe da suka shiga LUTH, babu Likitoci a kasa da zasu duba marasa lafiya.
"A jiya lokacin da na shiga asibitin, akwai marasa lafiya da dama. Babu Likitocin da zasu duba su saboda yajin aiki. Mutane na kwance sun shan wahala. ya kamata gwamnati ta shiga lamarin nan," yace.
"Kafin in bar wajen, an kawo wani mara lafiya cikin motar asibiti. Babu Likitoci, dole suka dauke mara lafiyan."
KU KARANTA: Yan sanda sun ceto mutum 15 da akayi garkuwa da su a jihar Kaduna
KU KARANTA: Bidiyon Boko Haram farfaganda ne, ba su suka harbo jirgin Soji ba: Binciken Masana
Wata ma'aikaciyar asibiri, Afeware Esther, wacce tayi magana madadin asibitin ta ce akwai tsarin da aka yi don tabbatar da cewa masu bukatar ganin Likita sun samu gani duk da yajin aiki.
"Muna da manyan Likitoci a kasa, ba zai yiwu a kori marasa lafiya ba. Ba zai yiwu mu kulle asibiti don rashin likitoci ba. Akwai malaman jinya," tace.
A bangare guda, gwamnatin tarayya zata tilasta dokar dakatar da albashi matsawar ma'aikaci bai yi aikinsa ba ga kungiyar likitoci masu neman kwarewa na Najeriya basu koma kan ayyukansu ba.
Ministan ayyuka da kwadago, Chris Ngige ne ya sanar da wannan jan kunnen a ranar Juma'a a wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels.
"A ranar Talata, zan gayyacesu don su koma kan ayyukansu. Zan sanar dasu cewa matsawar ba su yi aiki ba gwamnati ba za ta biyasu ba," cewar Ngige.
Asali: Legit.ng