Najeriya na gab da rugujewa gaba daya, Farfesa Attahiru Jega

Najeriya na gab da rugujewa gaba daya, Farfesa Attahiru Jega

  • Malamin makaranta kuma tsohon baturen zaben Najeriya ya bayyana cewa kasar nan na bukatar ceto na gaggawa
  • Jega wanda yace a ra'ayinsa, Najeriya na gab da rugujewa gaba daya saboda irin kidahuman shugabanninta dake jagoranci
  • Attahiru Jega ya yi kira ga masu kishin kasar nan su kawo mata dauki na gaggawa

Abuja - Tsohon Shugaban hukumar shirya zaben kasa watau INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa Najeriya na gab da rugujewa saboda ganganci da mulkin makafin da ake mata.

Jega ya bayyana hakan ne ranar Laraba a taron da kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta shirya a birnin tarayya Abuja, rahoton Vanguard.

Farfesa Attahiru Jega
Najeriya na gab da rugujewa gaba daya, Farfesa Attahiru Jega Hoto: INEC
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Mun yi ittifaki, Wajibi ne wanda zai gaji Buhari ya kasance Kirista daga kudancin Najeriya: CAN

A cewarsa, dubi ga yadda abubuwa ke gudana a kasar nan yanzu, da alamun zaben 2023 kadai zai iya bayyana halin da ranar goben kasar nan zata shiga.

A cewarsa,

"Ko da kasar bata gama rugujewa ba gaba daya, tana hanyar rugujewa saboda gangancin da masu mulki ke yi da kuma tukin makahon da ake wa kasar. Zaben 2023 zai bayyana halin da kasar ne zata shiga gobe."
"Saboda haka, akwai bukatar masu kishin kasa su hada karfi da karfe wajen ceto kasar nan daga rugujewa zuwa kasa mai shugabannin kwarai, cigaban kwarai, da tsaro ga 'yayanta."

Hukumar INEC ta sanar da ranar zaben shugaban kasa na 2023

Hukumar shirya zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta sanar da ranar da za'a gudanar da zaben shugaban kasa, yan majalisa da gwamnoni na shekarar 2023.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya sanar da hakan a hira da manema labarai ranar Asabar a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Niger: 'Yan ta'adda sun ragargaza garinsu sakataren gwamnatin jihar

A cewarsa, za'a gudanar da zaben Shugaban kasa da na majalisar dokokin tarayya ranar Asabar, 25 ga watan Febrairu, 2023.

Yayinda na gwamnoni da majalisar dokokin jiha zasu gudana ranar Asabar, 11 ga Maris, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel