Yanzu-yanzu: Hukumar INEC ta sanar da ranar zaben shugaban kasa na 2023

Yanzu-yanzu: Hukumar INEC ta sanar da ranar zaben shugaban kasa na 2023

  • Daga karshe, hukumar INEC ta sanar da sabon ranar da za'a gudanar da zaben shugaban kasa a 2023
  • Wannan ya biyo bayan rattafa hannu da Shugaba Buhari ya yiwa sabuwar dokar zabe
  • Dokar zaben na kunshe da sauye-sauye wanda ya hada da amfani da yanar gizo wajn tura sakamakon zabe daga rumfar zabe

Abuja - Hukumar shirya zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta sanar da ranar da za'a gudanar da zaben shugaban kasa, yan majalisa da gwamnoni na shekarar 2023.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya sanar da hakan a hira da manema labarai ranar Asabar a birnin tarayya Abuja.

A cewarsa, za'a gudanar da zaben Shugaban kasa da na majalisar dokokin tarayya ranar Asabar, 25 ga watan Febrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Mun yi ittifaki, Wajibi ne wanda zai gaji Buhari ya kasance Kirista daga kudancin Najeriya: CAN

Yayinda na gwamnoni da majalisar dokokin jiha zasu gudana ranar Asabar, 11 ga Maris, 2023.

Yakubu yace wannan sabon rana ya yi daidai da ka'idojin da doka ta gindaya na sanar da ranar zabe ana saura akalla kwanaki 260 da ranar zabe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wajibi ne wanda zai gaji Buhari ya kasance Kirista daga kudancin Najeriya: CAN

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta bayyana cewa ta yi ittifaki kuma ta yanke shawara kan matsayarta game da zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Shugaban CAN na kasa, Rabaran Samson Ayokule yace wajibi ne Shugaban kasa na gaba ya kasance Kirista daga kudancin Najeriya.

A cewarsa, CAN ba tada wani dan takara amma ba zata taba yarda Musulmi da Musulmi suyi takara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel