Sojin hadin gwiwa sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a iyakar Kamaru da Najeriya

Sojin hadin gwiwa sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a iyakar Kamaru da Najeriya

  • Rundunar hadin gwiwa ta sojoji ta hallaka 'yan ta'addan Boko Haram da dama a wata mafakarsu a iyakar Najeriya da Kamaru
  • Sanarwar da rundunar ta fitar ta bayyana sojojin suka kwato kayayyaki da yawa daga wajen 'yan ta'addan
  • Hakazalika, rahoton sojojin ya ce, an jikkata 'yan ta'addan da dama sun kuma gudu da raunuka daban-daban

N’Djamena, Chadi - Dakarun rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF) a Kamaru sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'addan Boko Haram da dama a yankin Vretet-Zamga-Ngoshe na Kirawa da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Babban jami’in yada labarai na rundunar sojin MNJTF da ke N’Djamena Chadi, Kanar Muhammad Dole, a wata sanarwa da ya fitar jiya Litinin, ya ce da yawa daga cikin maharan sun gudu da raunukan harbin bindiga.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja

'Yam ta'addan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannu
Rundunar soji ta ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a iyakar Kamaru da Najeriya | Hoto: prnigeria.com

Ya kuma ce an kwato kayayyaki masu tarin yawa hade da kayan abinci iri-iri yayin aikin da aka gudanar tsakanin ranakun 23 da 27 ga Fabrairu, 2022.

Ya ce ‘yan ta’addan na tara kayan abinci na watan Ramadan mai zuwa ne, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sanarwar:

“A yayin aikin, kayayyakin da aka kwato sun hada da bindiga kirar AK47 guda daya, mujallar AK47 guda daya, alburusai da dama na masu girman 7.62MM na musamman, kekuna 21, kakin BHT daya, gero buhu 39 da buhunan wake biyu.
“Binciken sirri ya nuna cewa ana safarar kayayyakin ne daga kan iyakokin kasar zuwa dajin Sambisa. An yi imanin cewa 'yan ta'addan na tara kayan azumin watan Ramadan mai zuwa ne.
“Karin bincike a wuraren da aka yi ragargazar ya nuna alamun jini, shaidan cewa 'yan ta'addan na BHT/ISWAP sun kwashe gawarwakin abokan aikinsu da suka mutu yayin da aka gano gawarwaki biyu na ‘yan Boko Haram.”

Kara karanta wannan

El-Rufai: Ni da wasu gwamnoni 5 za mu sayo na’urorin harba makamai daga Turkiyya don murkushe 'yan binidiga

Kwamandan rundunar ta MNJTF Manjo Janar Abdul Khalifah Ibrahim ya yaba wa sojojin, ya kuma bukace su da su jajirce WAJEN ci gaba da ragargazar 'yan ta'adda a yankin, Channels Tv ta ruwaito.

Borno: Hotunan yadda sojoji suka gargaji tarin 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP

A wani labarin, rundunonin sojin Najeriya, sun yi aikin share fage a wasu sassan jihar Borno, sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP a yayin aikin.

Rundunar 402 SF Brigade, a ranar 21 ga watan Fabrairu ne ta ragargaji 'yan ta'adda da dama a yankin Timbuktu Triangle a jihar Borno, inda ta kwato makamai da yawa ciki har da bama-bamai.

A bangare guda, rundunar 26 Task Force Brigade ta yi aikin sintiri tare da share maboyar 'yan ta'addan, lamarin da ya kai ga janyewar ISWAP/Boko Haram daga yankunan Fadagwe na da kewaye na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel