Abubuwa 8 da ya kamata ka sani game da ranakun zaben 2023 da INEC ta sanar

Abubuwa 8 da ya kamata ka sani game da ranakun zaben 2023 da INEC ta sanar

Hukumar shirya zaben kasa mai zaman kanta watau INEC a ranar Asabar ta sanar da sabbin ranakun gudanar da zaben shugaban kasa, gwamnoni da yan majalisu a 2023.

INEC ta yi wannan sanarwa ne biyo bayan rattafa hannun shugaba Buhari kan dokar zabe.

Wannan shine karo na hudu da aka yiwa dokar zaben gyaran fuska tsakanin 1999 da 2022.

INEC ta sanar
Abubuwa 8 da ya kamata ka sani game da ranakun zaben 2023 da INEC ta sanar
Asali: Original

Ga jerin abubuwa 8 da ya kamata ka sani game da zaben 2023 kamar yadda INEC ta sanar:

  • Wallafa sanar da ranar zabe - Litinin, 28 ga Febrairu, 2022
  • Zaben fidda gwani da rikice-rikicen da zai biyo baya - Litinin 4ga Afrilu zuwa 3 ga Yuni 2022
  • Mika takardun takara ga INEC ta yanar gizo na zaben Shugaban kasa na Majalisar dokokin tarayya - ranar Juma'a 10 ga Yuni zuwa Juma'a 17 ga Yuni 2022
  • Mika takardun takara ga INEC ta yanar gizo na zaben gwamnonin da Majalisar dokokin jiha - ranar Juma'a 1 ga Yuli zuwa Juma'a 15 ga Yuli 2022
  • Fara yakin neman zaben shugaban kasa da majalisar dokokin tarayya - Ranar 28 ga Satumba, 2022
  • Fara yakin neman zaben shugaban kasa da majalisar dokokin tarayya - Ranar 12 ga Oktoba, 2022
  • Ranar karshe na yakin neman zaben shugaban kasa da majalisar dokokin tarayya - 23 ga Febrairu, 2023
  • Ranar karshe na yakin neman zaben shugaban kasa da majalisar dokokin tarayya - 9 ga Maris, 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel