Fashola: Gwamnati za ta karasa manyan ayyukan da ta tattago kafin Buhari ya sauka

Fashola: Gwamnati za ta karasa manyan ayyukan da ta tattago kafin Buhari ya sauka

  • Babatunde Raji Fashola SAN ya yi alkawarin kammala hanyar Abuja-Kaduna-Kano nan da 2023
  • Ministan ya ce kafin Muhammadu Buhari ya tafi za a gama dagar Neja da hanyar Legas-Ibadan
  • Ministar kudi ta bayyana shirin Gwamnatin tarayya na kashe har Naira tiriliyan 1.4 a kan ayyuka

FCT, Abuja - Ministan ayyuka na kasa, Babatunde Raji Fashola SAN ya ce za a gama titin Abuja-Kano, da na Legas-Ibadan da gadar Neja nan da watanni 12.

A ranar Talata, jaridar Leadership ta rahoto Ministan ayyukan yana mai wannan bayani a wajen wani taron ganawa da jama’a da aka shirya a garin Abuja.

Ma’aikatar yada labarai da raya al’adu ta hada wannan taro kamar yadda ta saba yi domin bayyana irin nasarorin da gwamnatin nan mai-ci ta samu.

Kara karanta wannan

Alkali ya bada umarni hukumar EFCC ta karbe gidan tsohon Gwamnan APC a Abuja

Ministan ya ce ma’aikatarsa ta bada kwangilolin tituna 1, 018 na ayyuka 859 a jihohi 36 da garin Abuja. Jaridar nan ta Vanguard ta fitar da irin wannan rahoton.

Muhimman ayyuka 3

A cewar Ministan, gwamnatin tarayya za tayi kokari wajen ganin ta kammala duka wadannan manyan ayyuka kafin wa’adin Muhammadu Buhari ya cika.

Ana kokarin fadada titin Abuja-Kaduna-Kano wanda zai hada jihohin Arewacin Najeriya da birnin tarayya Abuja. A halin yanzu wannan aiki yana ta tafiya.

Aikin titi
Hanyar Legas zuwa Ibadan Hoto: www.julius-berger.com
Asali: UGC

Baya ga haka akwai babban titin Legas zuwa Ibadan wanda an dade da fara aikin. Sai kuma gadar nan ta 2nd Niger wanda ta hada 'Yan Neja-Delta da kasar Ibo.

Shirin da muke yi a 2022 - Zainab Ahmed

A wajen wannan taro, Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed ta samu damar yin jawabi, ta bayyana irin nasarorin da suka samu.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da Kwankwaso ya fada wajen kaddamar da sabuwar tafiyar siyasarsu

Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya ta fi maida hankali wajen kashe kudi a kan samar da abubuwan more rayuwa domin inganta tattalin arzikin kasa.

A wajen wannan taro, an ji cewa Najeriya za ta kashe kimanin Naira tiriliyan 1.42 a bana. Sannan gwamnati za a kashe Naira tiriliyan 2.11 wajen raya mutane.

EFCC v Okorocha

Dazu nan ku ka ji cewa hukumar EFCC ta fara samun nasara a kan Rochas Anayo Okorocha, Alkali ya bukaci a karbe wani gidan da ya mallaka a Abuja.

Hukumar EFCC ta na zargin cewa da kudin gwamnatin Imo aka saye gidan, don haka kotu ta ce a karbe gidan sai sun karkare shari’a a babban kotun tarayyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel