Kano: Gwamnati Za Ta Raba Wa Tubabbun 'Yan Shaye-Shaye Tallafin Tumaki Da Shanu

Kano: Gwamnati Za Ta Raba Wa Tubabbun 'Yan Shaye-Shaye Tallafin Tumaki Da Shanu

  • Hukumar Bunkasa Noma da Kiwo Ta Gwamnatin Tarayya, NALDA za ta bai wa tubabbun ‘yan shaye-shaye maza da mata 500 tallafin dabbobin kiwo a Jihar Kano
  • Sakataren hukumar, Prince Paul Ikonne ya bayyana hakan a wata takarda wacce ya saki a Abuja ranar Laraba inda yace cikin wadanda zasu amfana akwai maza 200 da mata 300
  • A cewarsa, dama an horar da wadanda za a ba dabbobin akan yadda za su gudanar da kiwo kuma su bunkasa sana’arsu ta yadda za su dogara da kawunan su

Jihar Kano - Hukumar bunkasa noma ta kiwo ta gwamnatin tarayya, NALDA zata bai wa tubabbun ‘yan shaye-shaye 500 tallafin dabbobin kiwo don su tsaya da kafafun su, Vanguard ta ruwaito.

Sakataren hukumar na kasa, Prince Paul Ikonne ya bayyana hakan ne ta wata takarda wacce ya saki a Abuja inda yace cikin tubabbun ‘yan shaye-shayen akwai maza 200 da mata 300 wadanda za su samu shanu da tumakin.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: An bayyana babban abin da zai tarwatsa jam'iyyar APC nan gaba kadan

Kano: Gwamnati Za Ta Raba Wa Tubabbun 'Yan Shaye-Shaye Tallafin Tumaki Da Shanu
Gwamnatin Kano Za Ta Raba Wa Tubabbun 'Yan Shaye-Shaye Tallafin Tumaki Da Shanu. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za a kammala kashi na farko ne a watan Maris inda ya kara da cewa yanzu haka cikin mata 100 ko wacce ta samu tumaki 3 yayin da matasa 200 suka samu shanaye bibbiyu.

Za a horar da wadanda za a bai wa dabbobin akan harkokin kiwo da sarrafa kudi don bunkasa kasuwancin su yadda ya dace.

NALDA, NDLEA da wata kungiya mai zaman kanta ne suka tsaya akan shirin

Ikonne ya ce NALDA ta hada kai da NDLEA ne da wata kungiya mai zaman kanta, Salamah Youth Empowerment and Enlightenment Initiative don tabbatar da shirin.

A cewarsa:

“Idan aka bar su babu sana’ar yi zasu koma shaye-shayen. Ta wannan hanyar ne zasu samu ababen yi wadanda zasu kawar da hankulansu daga shaye-shaye.
“Yanzu haka mun riga mun ba mutane 300 na kashin farko, za a raba wa sauran mutanen guda 200 dabbobin a watan Maris.”

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU za ta yi zaman farko da Gwamnatin Tarayya mako 1 da fara yin yajin-aiki

Ya bukaci sauran kungiyoyi su tallafa wa masu shaye-shaye wurin hana su harkar inda ya bayar da tabbaci akan yadda NALDA ta ke shirin kawo ci gaba ta harkar noma ta kiwo.

Ana sa ran idan suka juya wasu daban za su amfana

Ya yi bayani kamar yadda Vanguard ta ruwaito akan yadda suke sa ran wadanda aka ba dabbobin zasu sayar da su, su siya wasu sannan su yi amfani da ribar wurin harkokin rayuwarsu.

Ya ce kungiyoyin mahauta ne zasu tsaya tsayin-daka wurin tabbatar da an siyar da dabbobin yadda ya dace.

Ikonne ya ce za a juya kudaden yadda sauran mutane zasu amfana su daina shaye-shaye musamman matasa.

Ya kara da cewa:

“Matan da suka samu tumaki zasu kiwata su na watanni 6 zuwa shekara daya, ya danganta da girman su.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel