Bayan daure shi kan N2bn, Abdulrasheed Maina ya kamu da hawan jini da rashin jin magana

Bayan daure shi kan N2bn, Abdulrasheed Maina ya kamu da hawan jini da rashin jin magana

  • An cigaba da shari’a da Mista Abdulrasheed Maina a wani kotun tarayya da ke zama a Jabi-Abuja
  • Asibitin Uni Abuja sun aikowa kotu takarda, su na sanar da halin da Abdulrasheed Maina yake ciki
  • Likitan da ya rubuta takardar ya ce Maina yana da hawan jini da matsaloli a kunne da kuma kansa

Abuja - Tsohon shugaban hukumar PRTT da aka soke, Abdulrasheed Maina, ya na zuwa asibiti ana duba lafiyarsa, Premium Times ta fitar da wannan rahoto.

Ana yi wa Abdulrasheed Maina maganin larurar rashin jin sauti da kuma hawan jini a asibitin koyar da aikin likita da ke karkashin jami’ar tarayya ta Abuja.

Baya ga haka, asibitin sun bayyana cewa Maina wanda yake kan daurin shekaru takwas a gidan yari zai ga likita, an sa ranar da za ayi masa gwajin jin magana.

Kara karanta wannan

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

Bayan matsala a kunnuwansa, za a duba kwakwalkwalar Maina domin ayi wa gwajin lafiyarta.

Maina ya saci N730m?

Jaridar ta samu ganin wasikar da asibitin suka aikowa kotun tarayya da ke zama a Jabi, garin Abuja inda ake yin wata shari’ar da Maina kan zargin cin N738m.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abdulrasheed Maina
Abdulrasheed Maina a kotu Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Alkalin da yake sauraron wannan kara, Abubakar Kutigi ya yi magana a game da takardar, amma bai bayyana abin da ta kunsa ba a zaman da kotunsa tayi a jiya.

Maina bai samu zuwa kotun ba, lauyoyin da suka shigar da kara da wadanda suke kare shi, duk ba su iya yi wa Alkali Abubakar Kutigi bayanin inda ya shiga ba.

Rashin lafiyar Maina

Wani kwararren Likitan kunne a sashen ENT na asibitin na UniAbuja, Dr. I.O Omonua ya sa hannu a wannan takarda da ta fito ranar 18 ga watan Fubrairu 2022.

Kara karanta wannan

Dirama ta kaure yayinda wanda ake zargi da kisan dalibar UniJos ya haukace a kotu

Da yake bayanin halin da Maina yake ciki, Dr. I.O Omonua ya ce jami’in gwamnatin ya samu matsala da kunnuwansa, bai ji sosai a gefen kunensa na hagu.

Sannan kuma Likitan ya ce Mista Maina yana fama da hawan jini. Ko da an ba shi magungunan da za su taimaka masa, likitan ya ceana wasa da shan maganin.

Lauyan da yake bada kariya, Anayo Adibe ya nemi a saurari zuwan Maina, A karshe Alkali ya bukaci a tuntubi gidan yari a kan inda yake, kafin ya daga karar.

Ciwon kafar Maina

A lokacin da ake shari'ar farko da shi, an ji Abdulrasheed Maina ya shaidawa wani gidan rediyo cewa bai da lafiya. Maina ya bayyana cewa har an kwantar da shi.

Jami’in gwamnatin yace jinya ta hana shi fitowa yayin da ake nemansa. A cewarsa yana kwance domin kafarsa ta sa shi a gaba, hakan ta sa aka nemi shi aka rasa.

Kara karanta wannan

Sharri aka min, ina da ciwon sukari da hawan jini: Abba Kyari ya kai karar gwamnati kotu

Asali: Legit.ng

Online view pixel