Ina asibiti, bani da lafiya - Abdulrasheed Maina ya maida martani ga hukuncin Kotu
- Abdulrasheed Maina yayi magana da wani gidan rediyo daga inda ya ke kwance
- Tsohon jami’in gwamnatin yace jinya ta hana shi fitowa yayin da ake ta nemansa
- Ya zargi EFCC da rashin gaskiya, sannan yace an hana shi ganin shugaban kasa
Abdulrasheed Maina wanda ake nema a kotu ya fito ya bayyana cewa bai tsere ba, ya na nan ya na jinya asibiti, sannan ya fadi wasu abubuwa da ba a sani ba.
Maina ya ce: “Likita ya rubuta takarda cewa bani da lafiya, kafa ta ba lafiya, za ayi mani aiki, aka yi mani aiki, sai kawai ina zaune a asibiti na ji ana nema na.”
“Ana ta cigiya ta kamar ya?”
“Shi Sanatan da ya sa mani hannu, ‘dana ya fada masa ‘Ka zo muje ka ga mahaifina a asibitin da yake’, ya ki zuwa, kuma ya zai fada wa kotu bai san inda na ke ba?”
KU KARANTA: 'Danuwan Maina na jini ya roke shi ya fito, ya mika kan shi
Maina ya ce maganar Ali Ndme ba daidai ba ce, ko kuma wadanda suka fada masa sun yi masa karya.
Tsohon jami’in gwamnatin ya ke cewa: “Mu da muke gyara, zamu kawo gyara, muna taimakon kasa, an yi mana katanga da shugaban kasa, an bata mu.”
“An je ana amfani da EFCC a kanmu, wasu ma’aikatan EFCC da suka karbi kudin na sansu, idan lokaci ya yi zan fadi sunayensu, al’umma su sansu.” Inji Maina.
Abdulrasheed Maina ya tambayi ina N1.6tr da kuma N1.3tr da daruruwan gidaje da ya karbe daga hannun barayin gwamnati a lokacin Jonathan da shugaba Buhari.
KUU KARANTA: Kotu tana cigiyar Hon. ‘Dan Majailisa da Faisal Maina
Maina ya ce yana so ya so shugaban kasa ya san halin da ake ciki domin an yi masa shamaki da shi.
A karshe a hirar da aka yi da shi a gidan rediyo, tsohon shugaban kwamitin binciken kudin fansho na kasar, ba zai tsere ba, ya na nan a Najeriya yana jinya.
Mun ji cewa wata Ƙungiya ta matasan arewacin Najeriya ta yi tir da tsare Sanata Ali Ndume da aka yi a dalilin rashin bayyanar Abdulrasheed Maina a gaban kotu.
Kungiyar Arewar tayi mamakin ganin yadda Alkali ya bar Sanata Enyinna Abaribe ya yi tafiyarsa duk da ya kasa gabatar da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu a kotu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng