Da Dumi-Dumi: Yayan Babban Sarki A Arewa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Da Dumi-Dumi: Yayan Babban Sarki A Arewa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Yarima Samuel Ogwuche Akpa, yayan Attah na Igala, Mai Martaba Mathew Opaluwa Oguwche na 11 ya rasu
  • Samuel Ogwuche Akpa, ya rasu ne a yammacin ranar Litinin bayan fama da rashin Lafiya a garin Idah, Jihar Kogi
  • Majiyoyi daga fadar Attah na Igala sun tabbatar da rasuwarsa inda aka bayyana cewa rashin lafiya da ta same shi ne yasa ba shi aka zaba sarki ba

Jihar Kogi - Yarima Samuel Ogwuche Akpa, yayan Attah na Igala, Mai Martaba Mathew Opaluwa Oguwche na 11 ya rasu a ranar Litinin.

Daily Trust ta rahoto cewa ya rasu ne kwanaki 11 kafin bikin mika sandan mulki ga Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello zai bawa Attah na Igala.

Da Dumi-Dumi: Mai Martaba Attah Na Igala Ya Yi Babban Rashi
Da Dumi-Dumi: Yayan Attah Na Igala Ya Rasu. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Mulki ba naku bane: Obasanjo ya shawarci tsoffin da ke neman tsayawa takara a 2023

An ce an hangi marigayin a fadar Attah na Igala a hedkwatar masarautar Igala mai dimbin tarihi a ranar Lahadi, yana wasa da dariya tare da kaninsa, abin sha'awa.

Yariman, wanda ya yi takarar kujerar mulkin tare da kaninsa ya fara rashin lafiya ne a safiyar ranar Litinin kuma ya rasu da yamma, Daily Trust ta rahoto.

Ya rasu yana da shekaru 60 da yan kai, bayan rashin lafiya a Idah.

Majiya daga fadar Attah ta tabbatar da rasuwar Samuel Ogwuche

Wata majiya daga fada ta ce:

"Abin bakin cikin ya faru ne a yammacin ranar Litinin 21 ga watan Fabrairun 2022."

Majiyar Legit.ng ta gano cewa marigayin ya samu ciwon mutuwar rabin jiki.

"Idan ba domin ciwon ba, da shine zai gaji marigayi Attah na Igala, Micheal Idakwo Ame Oboni, wanda ya tafi farauta," in ji wani dattijo daga fada.

Kafin rasuwarsa a ranar Litninin, marigayi Sam, kamar yadda aka saba kiransa, tsohon ma'aikaci ne a babban bankin kasa, CBN.

Kara karanta wannan

Obasanjo: Abin Da Ƴan Boko Haram Suka Faɗa Min A Lokacin Da Muka Haɗu

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

A wani labarin, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel