Lauya ya wanke Pantami da Jami’ar FUTO a sa-in-sarsu da ASUU kan zamansa Farfesa

Lauya ya wanke Pantami da Jami’ar FUTO a sa-in-sarsu da ASUU kan zamansa Farfesa

  • A ra’ayin Iheanacho Agboti, babu yadda ASUU ta iya don an ba Isa Ali Pantami matsayin Farfesa
  • Barista Iheanacho Agboti ya ce a dokar kasa, ba kungiyar ASUU ke hukunta shugabannin jami’a ba
  • Lauyan ya fayyace abin da dokar kasa ta ce a kan wanda aka ba hurumin daukar mataki a kan jami’o'i

Ebonyi - Wani lauya mai suna Iheanacho Agboti da ke aiki a garin Abakaliki, jihar Ebonyi, ya yi magana a game da rikicin kungiyar ASUU da jami’ar FUTO.

Vanguard ta rahoto Barista Iheanacho Agboti ya ce a dokar aikin kasa wanda aka yi wa garambawul a shekarar 2005, babu yadda ASUU ta iya da jami’ar.

Masanin shari’ar ya ce dokar Trade Union (Amendment) ta 2005 ba ta ba kungiyar ASUU hurumin ta hukunta shugabannin jami’a idan su ka saba wata doka ba.

Kara karanta wannan

Kun mayar da lakcarori bayi: ASUU ta caccaki gwamnatin Buhari kan batun albashi

Lauyan ya bayyana wannan ne da yake magana da ‘yan jarida a garin Abakaliki domin yin karin haske a kan abin da doka ta ce a game da surutun da ake ta yi.

Barista Iheanacho Agboti ya caccaki kungiyar malaman jami’ar da shiga hurumin da ya fi karfinta.

Pantami
Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami Farfesa Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, majalisar da ke sa ido a kan harkar jami’a ce kadai dokar Universities Miscellaneous Provisions Act 2012 ta amince ta hukunta shugabannin jami’a.

“Ni Lauya ne, kuma gaskiya ita ce ASUU ba ta da hurumi a dokar ‘Nigerian Trade Union’ da za ta dauki mataki a kan shugabannin jami’ar FUTO a kan zargin saba doka.”
“Jahiltar gaskiyar lamarin da ASUU ta yi abin takaici ne. Babu inda a dokar Nigerian Trade Union aka yi wa kwaskwarima a 2005 da ta kyale ASUU ta hukunta jami’a.”

Kara karanta wannan

Yajin-aiki: Kafin magana ta yi nisa, Ministan ilmi na neman biyan bukatar kungiyar ASUU

Lauyan ya ce da wannan doka duk wata kungiya ta ke amfani. Haka zalika jami’o’i su na amfani ne da dokar Universities (Miscellaneous Provisions) (Amendment)

Jaridar ta rahoto Lauyan yana kira ga shugabannin kungiyar ASUU su ajiye maganar daukar mataki a kan jama’ar FUTO, ya ce ko su hakura ko a kai su kotu.

Pantami ya zama Farfesa

Zaman Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami Farfesa a jami’ar tarayya ta FUTO ya jawo surutai a Najeriya inda har ASUU ta ke zargin an saba doka wajen nadin mukamin.

A karshen 2021 ne Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya zama Farfesa a jami’ar tarayya da ke Owerri. Malamin ya na cikin wadanda aka tabbatar da karin matsayinsu.

Ministan sadarwan kasar Farfesa ne yanzu a fagen tsaron kafafar yanar gizo. Amma wasu su na ganin bai dace a nada shi Minista alhali ba ya koyarwa a jami'ar ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Kwamishinan Ganduje bai dandara ba, ya dawo Facebook daga barin kurkuku

Asali: Legit.ng

Online view pixel