Yajin-aiki: Kafin magana ta yi nisa, Ministan ilimi na neman biyan bukatar kungiyar ASUU

Yajin-aiki: Kafin magana ta yi nisa, Ministan ilimi na neman biyan bukatar kungiyar ASUU

  • Ministan ilmi ya dauki wani mataki da ake sa rai zai sa a dawo cigaba da koyar da dalibai a jami’o’i
  • Adamu Adamu ya karbi rahoton binciken da aka gudanar a makarantun gaba da sakandare a 2021
  • A halin yanzu kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta tafi yajin-aikin da zai dauki akalla wata guda

Abuja - Ma’aikatar ilmi ta tarayya ta fara kokari na ganin ta biya wani daga cikin bukatun da kungiyar malaman jami’a watau ASUU suka zo da shi.

Jaridar Punch ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na shirin aiki da rahoton kwamitocin da shugaban kasa ya nada domin su yi bincike a jami’o’in.

Darektan yada labarai na ma’aikatar ilmi, Ben Goong ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

ASUU ta dauki sama da shekara daya tana sauraron gwamnatin Muhammadu Buhari ta cika wannan alkawari da aka yi mata kafin ta dawo aiki a 2020.

Kara karanta wannan

Yadda manya suka yi kokarin wanke Abba Kyari daga badakaloli amma abin ya faskara

Kwamitocin da aka kafa za su duba matsalolin shugabancin da ake fama da su a jami’a. Daga nan kuma sai su bada shawarwari a kan yadda za a kawo gyara.

Ministan ilmi
Malam Adamu Adamu Hoto: 247ureports.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin Ben Goong

Sanarwar da ta fito daga bakin Ben Goong a ranar Alhamis ta ce babban Ministan ilmi, Adamu Adamu ya dauki mataki na gaba domin ganin an yi abin da ya dace.

“Bayan ya karbi rahoton kwamitocin da aka kafa a shekarar bara, Ministan ilmi, Adamu Adamu ya fitar da farar takarda na makarantun gaba da sakandare a fadin kasar nan.”
“An fitar da fararen takardu 10 na jami’o’i 36, yayin da aka fitar da shida na makarantun koyon sana’a da kuma takardu biyar na kwalejin ilmi 21.”
“Kowane kwamiti zai fitar da farar takarda na jami’o’i hudu. Za a rantsar da kwamitocin a ‘yan kwanaki masu zuwa.”

Kara karanta wannan

Karfin hali: An yi cacar baki tsakanin mai Shari'a da Nnamdi Kanu kan tufafinsa

“Dukkanin kwamitocin su na da makonni biyu daga lokacin da aka rantsar da su domin su gabatar da rahotanninsu.”

- Ben Goong

Jaridar ta nemi jin ta bakin shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, amma ba a same shi ba.

Shirin karkare N-Power

An ji Gwamnatin Muhammadu Buhari za ta ba dinbin matasan da za su kammala aikin N-Power jarin da zai ba su damar fara kasuwanci ko wata sana’a a Najeriya.

Ku na sane cewa a cikin matasa 500, 000 da za su gama N-Power bayan shekaru 2 su na cin albashi, an zabi fiye da rabi daga cikinsu wadanda CBN za ta ba jari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel