Tashin hankali: Mutane sun rasa rayukansu a kan hanyar dawowa daga wurin Jana'iza

Tashin hankali: Mutane sun rasa rayukansu a kan hanyar dawowa daga wurin Jana'iza

  • Yan bindiga sun harbe mutum uku har lahira a kan hanyarsu ta komawa gida daga halartar wurin Jana'iza a jihar Benuwai
  • Gwamnatin jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an kai gawar mutanen babban Asibitin Gbajimba, yankin Guma
  • Har yanzun hukumar yan sanda reshen jihar ba ta ce uffan ba game da lamarin, wanda ya faru ranar Asabar da yamma

Benue - Wasu tsagerun yan bindiga sun halaka aƙalla mutum uku da ke kan hanyar komawa gida daga halartar bikin Jana'iza a jihar Benuwai.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an kashe mutanen ne a kan hanyar Iordye zuwa Gbajimba, ƙaramar hukumar Guma ta jihar Benuwai.

Yan bindiga
Tashin hankali: Mutane sun rasa rayukansu a kan hanyar dawowa daga wurin Jana'iza Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Lamarin wanda ya lakume rayukan mutum uku, Maza biyu da kuma mace ɗaya, ya auku ne da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Yan bindiga sun kai kazamin hari, sun halaka mutane a jihar Benuwai

Gwamnatin jihar ta tabbatar

Kakakin gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, Nathaniel Ikyur, ya ce mutanen da lamarin ya shafa na cikin tafiya a Mota, lokacin da yan bindigan da ake zargin Fulani makiyaya ne suka farmake su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce ba zato ba tsammani maharan suka kai musu hari, suka bindige su har Lahira nan take a kan hanyar.

Kakakin gwamnan ya ƙara da cewa dakarun sojojin Operation Whirl Stroke sun ɗauko gawarwakin mutanen sun kai su ɗakin ajiye gawa na babban Asibitin Gbajimba, ƙaramar hukumar Guma.

Ya ce:

"Sojojin Operation Whirl Stroke sun ɗauke gawarwakin daga wurin zuwa ɗakin aje gawa na babban Asibitin Gbajimba."

Shin yan sanda sun samu rahoton aukuwar lamarin?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ba ta ɗaga kiran wayar salula da wakilan mu suka mata ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon daga da dan Basarake a Abuja, sun bindige mutum daya

Kazalika ba ta turo amsar sakonnin karta kwana da aka tura mata ba domin jin ta bakin hukumar yan sanda kan lamarin kamar yadda Sahara ta rahoto.

A wani labarin na daban kuma kun ji cewa Sabon Kwamishinan yan sanda da aka tura Katsina ya lashi takobin kawo ƙarshen ta'addancin yan bindiga

Sabon kwamishinan yan sanda a Katsina, CP Idrisu Dauda Dabban, ya shawarci yan ta'adda su tuba su miƙa wuya daga ayyukan sheɗanci kafin dakarun yan sanda su iso gare su.

Dabban, yace dakarun yan sanda za su yi aiki tukuru da taimakon Allah wajen kawo karshen ta'addanci a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel