Takardun kotu sun fallasa marigayin janar din sojan da EFCC ta kwace kadarorin N10.9b

Takardun kotu sun fallasa marigayin janar din sojan da EFCC ta kwace kadarorin N10.9b

  • Wasu takardun kotu sun bayyana sunan Marigayi Janar Aminu Kano Maude a matsayin babban sojan da EFCC ta kwace kadarorin N10.9b daga iyalansa
  • Duk da EFCC ta ki bayyana sunan babban sojan da aka kwace dukiyar daga hannunsa, ta nemi kautar da hankalin jama'a inda ta ambaci marigayin matsayin mai juya dukiyar
  • Babbar alkalin kotun tarayya da ke zama a Abuja ta bukaci karbe kadarorin da suka hada da gidajen mayuka a jihohin Kano, Borno da sauran kadarori na manyan kudi

Wasu takardun kotu kai tsaye ta alakanta kadarorin da hukumar EFCC ta kwace, wadanda suka kai darajar biliyan N10.9 da ake zargin an same su ta hanyoyin da basu da ce ba, daga hannun marigayi Janar din sojoji, Aminu Kano Maude.

Takardu kotun da Premium Times ta samu, ya cire rudanin alakanta kadarorin da ga wani "babban jami'in soja" a takardu biyun da Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta dade da fitar wa a kan kwace kadarorin.

Kara karanta wannan

Adashin N2,000 take kullum: Jami'ai kan mabaraciyar da aka kama da N500,000 da $100 a Abuja

Takardun kotu sun fallasa marigayin janar din sojan da EFCC ta kwace kadarorin N10.9b
Takardun kotu sun fallasa marigayin janar din sojan da EFCC ta kwace kadarorin N10.9b. Hoto daga @officialefcc
Asali: Twitter

Ba tare da bayyana sunan babban jami'in sojin ba, takardar da EFCC ta fitar ta kara da bayyana yadda "abokanan harkallar sojan da basu fadi sunansa ba ke jujjaya kadarorin, wadanda suka hada da; marigayi Janar Aminu Maude, kamfanoni irin su Atlasfield Integrated Services Nigeria Limited, Marhaba Event Place, Aflac Plastics da Atlasfield Gas Plant Limited."

Hukumar ta bibiyi takardar a washe garin ranar - 15 ga watan Fabrairu, inda ta cire sunan Maude gaba daya, sannan ta cigaba da cewa kadarorin "mallakin wani babban jami'in rundunar sojin Najeriya ne".

Dayar takardar, wacce ta bayyana jerin sunayen kadarori 24 da hukumar ta samu umarni daga babban kotun tarayya ta Abuja na kwace wa daga karshe a ranar Litinin, sun ce kadarorin sun kai na kimanin biliyan N3 da aka nuna a takardar farko amma daga bisani takardar ta biyu ta ce sun kai na biliyan N10.9.

Kara karanta wannan

Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari

Kakakin hukumar, Wilson Uwujaren ne yasa hannu a duka takardun biyu, don janye hankali daga kan Maude, a matsayin wanda ake zargi da mallakar kadarorin ta hanyar kwasar kudin kasa.

Kwafin takardar umarnin da alkalin babban kotun tarayya, Nkeoye Maha, ta bayar a ranar 13 ga watan Mayun 2020, na kwacee kadarorin na wuci-gadi, sai dai hakan ya alakanta kadarorin da ayyukan wawurar kudin kasar nan da Maude yayi.

Umarnin kotun, wanda ke dauke da taken da EFCC ta samar na umarnin kwace kayan na wucin gadi, ya ce, "bisa bukatar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ( EFCC) ya mika na umarnin kwace kadarorin na wucin gadi, duba da yadda wasu kadarorin suke a sassa daban-daban na fadin Najeriya, wadanda ake zargin janar Maude Aminu Kano da abokanshi na kamfanoni da mutane sun mallaka ta hanyar damfara."

A umarnin da alkalin ya bada ya tafi ne kai tsaye ga EFCC na tallata umarnin kwace kadarorin a jaridu kuma duk wanda ya ga hakan bai masa ba da ya garzayo domin bayyana dalilansa.

Kara karanta wannan

EFCC ta bayyana kadarori 24 masu darajar N10.9bn da ta kwace wurin hadimin NSA Monguno

Kotun ta yi umarni da gayyatar koma waye dake da gamsassun hujjoji gaban kotun tarayya da zasu sa a soke umarnin karshe na kwace kadarorin, da ya bayyana gaban kotun don bayyana dalilan.

Haka zalika, Alkali Maha ta umarci EFCC da kada ta wuce kwana bakwai bata fitar da takardar biyayya da tallata umarnin kwace kadarorin na wucin gadi ba.

EFCC ta bayyana kadarori 24 masu darajar N10.9bn da ta kwace wurin hadimin NSA Monguno

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, a ranar Talata ta bayyana jerin kadarorin da ta kwace daga wani babban hafsan soja a kasar nan.

Kadarorin 24 sun kai darajar N10.9 biliyan, inda ya karu a kan kadarorin N3 biliyan da hukumar ta fara sanarwa a ranar Litinin.

Wani alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Mai shari'a Nkeoye Mana, ya bayar da umarnin kwace kadarorin kuma a mayarwa gwamnatin tarayya a ranar Litinin, kamar yadda Wilson Uwujaren, kakakin EFCC ya sanar.

Kara karanta wannan

Daga Sarki ya zama Bawa: Rayuwar Abba Kyari a baya kadan da kuma yanzu

Asali: Legit.ng

Online view pixel