Rikicin APC a Daura: Shugaban jam'iyya na jihar ya yi fashin baki

Rikicin APC a Daura: Shugaban jam'iyya na jihar ya yi fashin baki

  • Shugaban jam'iyyar APC a Katsina yace babu wanda zai yi murdiyan dan takara a zaben shugabannin kananan hukumomi
  • Jawabinsa ya biyo bayan rahotannin rikici a garin Daura, jihar Katsina
  • Yayin da ake ta shirye-shiryen zaɓen kananan hukumomi a Katsina, rikici ya barke a jam'iyyar APC reshen Daura

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Katsina, Muhammad Sani Alu, ya yi fashin baki kan rikicin da ya barke a garin Daura, mahaifar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kun ji cewa fusatattun mambobin APC a karamar hukumar Daura, jihar Katsina sun ja daga kan zargin ƙaƙaba musu ɗan takarar kujerar ciyaman.

Shugaban ƙungiyar tsofaffin Kansiloli reshen jihar, Alhaji Ibrahim Suleiman, ya yi zargin murdiya a zaɓen fidda gwani.

Ya yi zargin cewa zaben fidda gwamnin da aka gudanar, wani Alhaji Shehu Abdu, shi aka bayyana ya lashe zaɓen, amma aki masa fin ƙarfi aka maye gurbinsa da Bala Musa wanda ɗan uwa ne ga tsohon shugaban hukumar tsaron farin kaya, DSS, Lawal Musa Daura.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Rikici ya barke a mahaifar shugaba Buhari Daura kan wanda za'a ba takara a APC

Amma Daily Trust ta ruwaito Shugaban jam'iyyar APC na jihar da cewa har yanzu Abdu ne dan takarar kuma tuni an tura sunansa wajen hukumar zaben jihar.

A kan tuhume-tuhumen da ake yiwa Abdu, Shugaban APC yace lamarin na kotu.

Shugaban jam'iyya na jihar
Rikicin APC a Daura: Shugaban jam'iyya na jihar ya yi fashin baki Hoto; Daily Trust
Asali: Facebook

Ina wanda ya samu nasarar yake?

Suleiman ya bayyana cewa wanda ya samu nasara a zaɓen yanzu haka yana karkashin bincike, kuma kwamishinan shari'a na da hannu a matsalar da aka jefa mutumin.

Ya ce an jefa Alhaji Shehu Abdu cikin matsala, an laƙaba masa zargin cewa ya karbi kuɗi hannun matasa da sunan zai samar musu aiki.

A cewarsa:

"Yanzu haka yana tsare a ofishin CID na jihar Katsina, muna tattauna wa da lauyoyin mu kan yadda zamu ɗauki lamarin. Abun takaici haka na faruwa a mahaifar Buhari."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya soke taronsa da gwamnonin APC bayan sun hallara, zai shilla turai

"Matsalar na nema zama babbar barazana ga jam'iyya domin alama ce ta hatsari babba yayin da ake fuskantar zaɓen 2023."

Martanin Kwamishanan Shari'a

Amma kwamishanan shari'ar jihar, Ahmad El-Marzuq, ya karyata zargin da ake masa cewa yana da hannu.

Yace an damke dan takaran APC ne saboda kararsa da aka kai wa kwamishanan yan sanda.

A cewarsa:

"Dukkan zarge-zargen da ake min karya ne. Na farko, ba ni da dan takara; kuma kowa ya san Shehu Abdu ya shahara da damfarar mutane a karamar hukumar."
"Wadanda ya damfara a kauyukan dake Daura suka shiga da kararsa wajen kwamishanan yan sanda kuma aka bani cewa ya karbi kudi hannunsu daga N100,000, N50,000 dss."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel